'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari kan Shingen Binciken Ƴan Sanda, An Rasa Rayuka

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari kan Shingen Binciken Ƴan Sanda, An Rasa Rayuka

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an ‘yan sanda yayin aikin bincike a Rivers, inda suka kashe jami’ai biyu tare da raunata wani
  • Jami’an da abin ya shafa suna gudanar da aikin tsaro ne a wani shingen bincike da ke Obiri-Kwere, Obio/Akpor lokacin da aka farmake su
  • Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da harin tare da fara bincike domin gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki kan jami'anta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rivers - Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu tare da jikkata wani jami’i a yankin Obiri-Kwere da ke karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar Rivers.

Lamarin ya faru ne a daren Litinin yayin da jami’an ke gudanar da aikin bincike da tsaro a yankin.

'Yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda a Rivers
Motar sintirin 'yan sanda da wasu jami'an rundunar sun aikin bada tsaro. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda

Kara karanta wannan

Fusatattun dalibai sun rufe kofa, sun hana shugaban jami'a shiga cikin makaranta

Rahoton Punch ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan uku suna aiki ne a karkashin rundunar Aluu Division da ke karamar hukumar Ikwerre ta jihar.

An ce suna gudanar da aikin tsayar da ababen hawa da gudanar da bincike a wani shingen tsaro da ke hanyar Mbodo/Aluu a Obiri-Kwere Road lokacin da maharan suka bude musu wuta da misalin karfe 9:0 na dare.

Bayan harin, ‘yan bindigar sun gudu da motarsu, kamar yadda rahoton ya nuna.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, Blessing Agabe, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Ta ce jami’ai biyu sun rasa rayukansu, yayin da na ukun da ya samu mummunan rauni yake karbar magani a asibiti.

Ta ce:

“Eh, zan iya tabbatar da hakan. Mutane biyu daga cikin jami’anmu sun mutu, yayin da dayan ya samu rauni kuma yana asibiti yana karbar magani.”

Kwamishinan ‘yan sanda ya ziyarci wurin

Agabe ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Rivers, Olugbenga Adepoju, tare da manyan jami’an rundunar sun ziyarci wurin da harin ya faru domin duba halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane

Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata laifin, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Wannan harin ya faru ne kasa da sa’o’i 24 bayan rundunar ‘yan sandan Rivers ta sanar da cafke wani da ake zargi da aikata manyan laifuffuka mai suna Austine Emenike, wanda ake kira “Oyibo”.

‘Yan sanda sun ce wanda aka kama yana da alaka da wata babbar kungiyar masu aikata laifuffuka a jihar.

'Yan sanda sun fara bincike don kamo 'yan bindigar da suka kashe jami'anta a Rivers.
Taswirar jihar Rivers, inda 'yan bindiga suka kashe jami'an 'yan sanda
Source: Original

Bidiyo ya nuna gawarwakin jami’an

Wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna gawarwakin jami’an suna sanye da kayan aikinsu a wurin da aka kai harin.

Wata murya a cikin bidiyon ta yi ikirarin cewa ‘yan fashin ne suka kai hari a yankin kafin su bude wuta kan jami’an tsaron.

'Yan bindiga sun shammaci 'yan sanda

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa bayan da suka farmaki jami'an 'yan sanda a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma.

Tsagerun 'yan bindiga wadanda suka kasance masu dumbin yawa, sun yi harbe-harbe kan mai uwa da wabi bayan da suka farmaki jami'an 'yan sandan.

Harin da 'yan bindiga suka kai a wani shingen bincike ya jawo an samu asarar rayukan jami'an 'yan sanda tare da kona kayan da suke amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com