Bankin Duniya Zai ba Kano da Wasu Jihohi 4 Kyautar Dala Miliyan 15 saboda Kokarinsu

Bankin Duniya Zai ba Kano da Wasu Jihohi 4 Kyautar Dala Miliyan 15 saboda Kokarinsu

  • Kano, da wasu jihohin Najeriya za su samu kyautar dala miliyan 15 daga Bankin Duniya sakamakon nasarar aiwatar da sauye-sauyen ilimi da lafiya
  • Tallafin na cikin shirin HOPE Governance Programme da Bankin Duniya ke gudanarwa, don bada tallafin kudi ga jihohin da suka yi rawar gani
  • Jimillar dala miliyan 27 aka ware domin bai wa wasu jihohin Najeriya da suka cika sharuddan shirin tallafin bisa tsarin sakamakon da suka wallafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jihohi biyar na Najeriya za su karɓi jimillar dala miliyan 15 a matsayin tallafin ƙarfafa gwiwa bisa nasarar da suka samu wajen aiwatar da muhimman sauye-sauye a bangaren ilimi da kiwon lafiya.

Tallafin yana karkashin HOPE Governance Programme, wani shiri ne da Bankin Duniya ke gudanarwa na bada tallafi karkashin ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki ta tarayya.

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Bankin Duniya ya ba wasu jihohin Najeriya tallafin dala miliyan 15.
Getty Images
Source: UGC

Jihohin Najeriya da suka yi fice

Mai kula da shirin na kasa, Assad Hassan, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja yayin wani taro da kwamishinonin jihohi, sakatarorin dindindin da daraktocin kasafin kuɗi da tsare-tsare daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, in ji rahoton Punch.

Bayani daga jami’in hulɗa da jama’a na shirin, Joe Mutah, ya ce jihohin da suka fi samun damar tallafin su ne:

Dala miliyan 27 aka ware gaba ɗaya

Shirin HOPE Governance ya amince da bayar da jimillar dala miliyan 27 ga jihohin da suka samu nasara wajen cika sharuddan matakin farko na shirin, wanda ake kira Year Zero Disbursement-Linked Results.

An kafa wannan tsarin ne bisa rahoton wani kwamitin tantancewa mai zaman kansa wanda ya duba yadda jihohi suka cika wasu muhimman ka’idojin shirin.

Jihohin Bayelsa, Borno, Kano, Kebbi da Yobe za su samu dala miliyan 1.5 kowanne saboda cika sharuddan bangaren ilimin bai ɗaya.

Kara karanta wannan

Kano: An gano abin da ya jawo mummunan arangama tsakanin manoma da makiyaya

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wannan ya shafi samar da cikakkun tsare-tsare da jagororin shirya da gabatar da kasafin kuɗin ilimin firamare na jihohi.

Haka kuma, jihohin guda biyar za su sake samun karin dala miliyan 1.5 kowanne saboda cika sharuddan bangaren kula da lafiya matakin farko.

Wasu jihohi ma sun samu tallafi

A wani bangare na shirin, jihohi tara sun cancanci samun dala 500,000 kowanne saboda amincewa da tsarin kasafin kuɗi na kananan hukumomi da kuma tsarin lissafin kudade.

Jihohin sun hada da:

Shirin ya ce manufarsa ita ce karfafa shugabanci mai inganci da inganta yadda ake amfani da kudaden jama’a wajen samar da ayyukan ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com