Kasar Saudiyya Ta Kama Baƙin Haure 14,782 Cikin Mako Guda
- Kasar Saudiyya ta kama mutane 14,782 da suka karya dokokin zama, aiki da tsaron kan iyaka cikin mako guda
- An kama mutane 1,450 yayin da suke ƙoƙarin shiga Saudiyya ba bisa ka'ida ba, mafi yawansu 'yan Habasha da Yemen
- Ma'aikatar Cikin Gida ta gargadi masu taimaka wa bakin haure, cewa za su fuskanci hukuncin daurin shekara 15 da tarar Riyal miliyan daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
RIYAD — Hukumomin tsaron Saudiyya sun kama mutane 14,782 da ake zargi da karya dokokin zama da shigowa kasar ba bisa ka'ida ba cikin mako guda.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta ce an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro da hukumomin gwamnati da abin ya shafa tsakanin 10 zuwa 16 ga Satumba.
An kama masu karya dokokin Saudiyya
Daga cikin wadanda aka kama akwai mutane 7,438 da suka karya dokar zama a kasar, yayin da 3,782 suka karya dokar tsaron kan iyaka.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa cikin kasuwa ɗauke da makamai, rayukan bayin Allah sun salwanta
Haka kuma, an kama mutane 3,562 da suka karya dokar aiki ta kasar, kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana a ranar Lahadi.

Source: Getty Images
Ma'aikatar ta ce an mayar da bakin haure 12,635 zuwa kasashensu, yayin da aka tura 18,986 daga cikin wadanda aka kama zuwa ofisoshin jakadancinsu domin samun takardun tafiya.
Wasu mutane 3,834 kuma an tura su domin kammala shirye-shiryen tafiyarsu daga kasar kamar yadda aka saba duk lokacin da aka yi kame.
'Yan Yemen da Habasha sun fi yawa
Hukumomin sun kuma kama mutane 1,450 da ake zargi da ƙoƙarin shiga Saudiyya ta kan iyaka ba bisa ka'ida ba.
Daga cikinsu, 43% 'yan Yemen ne, yayin da 56% 'yan Habasha ne. Sauran 1% kuma sun fito ne daga wasu ƙasashe.
Haka kuma, an kama mutane 25 yayin da suke ƙoƙarin ficewa daga Saudiyya ba bisa ka'ida ba.
Bugu da ƙari, an kama mutane 23 da ake zargi da taimaka wa masu karya doka ta hanyar ba su sufuri, matsuguni ko aikin yi.
A halin yanzu, baki 31,075, ciki har da maza 29,171 da mata 1,904, suna fuskantar matakan shari'a saboda karya dokokin kasar.
Gargadi ga masu taimaka musu
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta yi gargadin cewa duk wanda ya taimaka wajen shigar da mutum cikin kasar ba bisa ka'ida ba, ko ya kai shi wani wuri, ya ba shi matsuguni ko kuma ya samar masa da wata hanya ta taimako, zai fuskanci hukunci mai tsauri.
A cewar ma'aikatar, wanda aka samu da laifin na iya fuskantar hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari da tarar da za ta kai Riyal miliyan daya.
Haka kuma, za a iya ƙwace motocin da aka yi amfani da su wajen safarar masu karya dokar ko gidajen da aka ba su matsuguni.
Ma'aikatar ta bukaci jama'a da su kai rahoton duk wani mai karya doka ta hanyar kiran lambar 911 a yankunan Makkah, Riyadh da yakin gabashin kasar.
A sauran yankunan kasar kuma, jama'a na iya kiran 999 ko 996 domin kai rahoton irin wadannan laifuka da Saudiyya ke kokarin magancewa.
Asali: Legit.ng
