Yadda Matasan Najeriya Za Su Nemi Aiki a Hukumar FRSC daga Ranar 3 ga Yuli

Yadda Matasan Najeriya Za Su Nemi Aiki a Hukumar FRSC daga Ranar 3 ga Yuli

Abuja - Hukumar FRSC ta sanar da fara aikin ɗaukar sababbin ma’aikata na shekarar 2026, inda ta buɗe damar ga ’yan Najeriya da suka cancanta su nemi guraben aiki a sassa daban-daban na hukumar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FRSC ta bayyana cewa masu sha'awar neman aikin za su fara cike fom din a shafinta daga ranar Juma’a, 3 ga Yuli, 2026, kuma za a ci gaba da hakan na tsawon makonni huɗu.

Hukumar FRSC za ta bude shafin daukar ma'aikata a ranar Juma'a
Jami'an hukumar FRSC suna gudanar da faretin karshen wata. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

FRSC za ta bude shafin daukar aiki

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar ɗaukar aikin mai kwanan wata 24 ga Yuni, wadda mataimakiyar kwamandan hukumar kuma shugabar sashen gudanarwa, Pauline Olaye, ta sanya wa hannu, in ji rahoton Punch.

Sanarwar wadda aka fitar a madadin shugaban hukumar FRSC na kasa, ta bayyana cewa cike fom din neman gurbin aikin kyauta ne.

Kara karanta wannan

INEC ta fara daukar ma'aikata domin zaben gwamnan Osun na 2026

“Babu wani kuɗi da ake biya wajen neman aikin,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ce masu sha’awar neman aikin za su gabatar da takardunsu ta shafin ɗaukar aikin hukumar na yanar gizo, sannan za a bukaci waɗanda aka zaɓa su zo da kwafin takardar neman aikin da suka cike yayin tantancewa.

Matakan aikin da FRSC ke nema

FRSC ta bayyana cewa ɗaukar aikin ya ƙunshi manyan sassa uku, watau Officer Cadre, Marshal Inspectorate Cadre da Road Marshal Assistant Cadre.

  • Officer Cadre

A ɓangaren Officer Cadre, hukumar na neman jami’an Superintendents Route Commanders, Route Commanders/Deputy Route Commanders da kuma Assistant Route Commanders.

Masu digiri kamar likitoci, malaman magani, ma’aikatan jinya, masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, lauyoyi, injiniyoyi da waɗanda ke da B.Sc, BA ko HND za su iya nema gwargwadon matsayin da suke nema. Yawanci masu wannan rukuni dole ne shekarunsu su kasance tsakanin 18 zuwa 35.

  • Marshal Inspectorate Cadre

A bangaren Marshal Inspectorate Cadre, masu takardun NCE, ND/OND, RN/RM da CHEW ne za su iya nema. Ana buƙatar shekarun masu nema su kasance tsakanin 18 zuwa 30.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

  • Road Marshal Assistant Cadre

Shi kuwa Road Marshal Assistant Cadre, an buɗe shi ga masu aƙalla maki uku a SSCE ciki har da Ingilishi da Lissafi, da kuma masu sana’o’i da direbobi.

Hukumar ta ce masu sana’o’i irin su masu aikin kwamfuta, gyaran mota, aikin lantarki, masu aikin famfo, tela, masu tuka babura da direbobi na iya nema idan suna da takardun cancanta na sana’arsu.

Masu neman matsayin direba ko mai tuka babur dole ne su kasance da ingantaccen lasisin tuƙi da ya dace. Direbobin manyan motoci masu ɗaukar kaya da na jan mota kuma dole ne shekarunsu su kasance tsakanin 26 zuwa 40.

Sharuddan da ake buƙata

FRSC ta bayyana wasu ƙarin sharudda ga masu neman aikin, ciki har da kasancewa ɗan Najeriya ta haihuwa, iya amfani da kwamfuta, samun lafiyar jiki da kuma kasancewa mara aure.

Hukumar ta ce dole ne mazan da za su nemi aiki su kasance masu tsayin aƙalla mita 1.65, yayin da mata kuma ake son masu tsayin da bai gaza mita 1.58 ba.

Kara karanta wannan

Babbar mota ta burma kan 'yan APC suna tafiya kamfen, an samu asarar rai

Ta kuma buƙaci masu nema su bayyana dukkan takardun karatu da cancantar da suke da su tun lokacin neman aiki, domin ba za a amince da takardun da ba a bayyana ba a gaba.

FRSC ta ƙara da cewa masu neman aiki za su kasance masu kyakkyawan hali, ba su da matsalar bashi, kuma ba su taɓa samun hukunci kan wani laifi ba.

Haka kuma, hukumar ta ce ba za ta saurari masu zanen tattoo a jiki ba, sannan ta shawarci masu nema su yi amfani da adireshin imel da lambar wayarsu ta kansu wajen aikawa da takardu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com