
Sani Hamza
3960 articles published since 01 Nuw 2023
3960 articles published since 01 Nuw 2023
Ana zargin mawaki Ali Jita da amfani da baitocin Yakubu Musa a wakarsa ta Amarya, lamarin da ake ganin zai iya kai shi gaban kotu bisa zargin satar fasaha.
Fitaccen jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya fara rigima da masu kallon Izzar So kan zargin shirin ya yi tsawo da yawa. Ya mayar da martani mai zafi, ciki har da zagi.
Tace fina-finai a Kano na kare tarbiyya da addini, amma masana da ’yan fim na ganin hakan na tauye fasaha da ’yancin fadin albarkacin baki da kuma dakile Kannywood.
Kano ta haramta haska fina-finai 22 na Kannywood saboda sabawa da al’adu, lamarin da ke haifar da ce-ce-ku-ce. Fina finan da aka hana haskawa sun hada da Labarina.
Hafsat Tuge ta kare 'yan Kannywood kan cewa ba su dace da aure ba. Ta ce suna aure kuma suna girmama mazajensu yayin da ta ce babu shirin aure a gabanta yanzu.
Rahama Sadau ta yi wa Yusuf Lazio sha tara ta arziki da ta gigita shi, inda ya gode mata tare da kiranta 'uwa', kuma ya roƙa mata albarka bisa karamcinta.
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da Samha M. Inuwa da Soja Boy bisa laifin tsiraici da batsa a bidiyo, tare da kwace lasisinsu. Mun yi bayani kan jaruman.
Masu kallo sun roƙi a cire Firdausi Yahaya daga shirin Jamilun Jiddan, duk da haka ta zama fitacciya a fina-finai da ta samu kambun "Jaruma Mai Tasowa."
Usman Soja Boy ya ce Kannywood ba ta tsinana masa komai ba. Ya yi zargin shi ne ke taimakawa masana’antar, kuma dakatarwar ba za ta wani dame shi ba.
Sani Hamza
Samu kari