Ana Rigimar Iran, Trump Ya Karbi Ragamar Juya Yankin Wata Kasa a Duniya
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington ta cimma yarjejeniya da Denmark da Greenland wadda za ta bai wa Amurka ikon dindindin kan tsaro da sauran bukatun yankin
- Trump ya ce yarjejeniyar za ta hana abokan gaba na Amurka kafa sansanonin soji ko jibge jami’an soji a Greenland ba tare da rubutaccen izinin Washington ba
- Sai dai Denmark da Greenland sun ce yarjejeniyar za ta mutunta ikon mallakar yankin da kuma ’yancin al’ummar Greenland na yanke shawara kan makomarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta cimma yarjejeniya da Denmark da Greenland da za ta ba ta ikon dindindin kan tsaro da sauran bukatun Greenland.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a ranar Juma’a, inda ya ce yarjejeniyar ta warware dukkan damuwar Amurka kan tsaron yankin.

Source: Getty Images
Amurka ta samu iko a Greenland
A sakon da ya wallafa a X, Trump ya ce Amurka za ta samu cikakken ikon yin duk abin da ta ga ya dace domin kare tsaron Greenland da na Amurka.
Ya kuma ce za a hana duk wani abokin gaba na Amurka kafa sansanin soji ko jibge jami’an soji a Greenland, sai dai idan ya samu rubutaccen izini daga Washington.
Shugaban na Amurka ya kuma ce za a fara shirye-shiryen gina babbar cibiyar soji a wuraren da suka dace a Greenland, yana mai cewa akwai wurare da dama da za a iya amfani da su.
Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani abu da ya dade yana fatan samu ga Amurka.
Maganar Denmark da Greenland
Gwamnatin Denmark da ta Greenland sun fitar da sanarwar hadin gwiwa ranar Juma’a, inda suka ce ana sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya na mako mai zuwa.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC
Sai dai yarjejeniyar za ta bukaci amincewar majalisun dokoki na Nuuk da Copenhagen kafin ta fara aiki.
Firaministar Denmark, Mette Frederiksen, ta ce yarjejeniyar ta amince da ikon mallakar Masarautar Denmark da mutuncin yankinta, tare da mutunta ’yancin al’ummar Greenland na yanke shawara kan makomarsu.
Firaministan Greenland, Jens-Frederik Nielsen, ya ce yarjejeniyar za ta ƙarfafa tsaron Greenland da Denmark, Amurka da ƙawancen kasashen Yamma.

Source: AFP
Me Amurka za ta yi a Greenland?
Al Jazeera ta wallafa cewa Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce yarjejeniyar ta magance damuwar Washington kan tsaron Greenland gaba ɗaya.
Rubio ya ce Greenland za ta kasance wani bangare na yankin da ke da muhimmanci ga tsaron Arewacin Amurka, tare da hana duk wani abokin gaba samun sansanin soji a yankin da kewaye.
Rahotanni sun bayyana cewa Amurka ta riga ta samu manyan hakkokin zirga-zirgar jiragen sama da amfani da sansanonin soji a Greenland tun bayan yarjejeniyar da ta kulla da Denmark a shekarar 1951.
Koriya ta gargadi Amurka
A wani labarin, kun ji cewa babbar jami’a a gwamnatin Koriya ta Arewa, Kim Yo Jong, ta yi gargadin cewa Pyongyang za ta mayar da martani mai ƙarfi ga atisayen soji da Amurka ke jagoranta a yankin Asiya da Pasifik.
Kim, wadda ’yar uwar Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ce, ta zargi Washington da kasancewa babban abin da ke ƙara tsananta rikicin yankin.
Ta yi magana ne musamman kan atisayen Pacific Vanguard 2026, wani atisayen sojin ruwa da Amurka, Koriya ta Kudu, Japan da wasu ƙasashe ke gudanarwa a kusa da Guam.
Asali: Legit.ng

