Akwai Dalili: Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatun Sakandare na JSS, SSS
- Gwamnatin Tarayya ta ce za ta soke tsarin raba ƙanana da manyan sakandare bayan gano ɗalibai sama da miliyan 20 sun daina karatu
- Ministan ilimi na Najeriya, Tunji Alausa ya ce tsarin JSS da SSS ya gaza cimma manufarsa tare da jawo cunkoso a wasu makarantu
- Gwamnati ta kafa kwamitin sa ido kan makarantun zamani domin tabbatar da kammala ayyukan da UBEC ta gina a faɗin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kawo ƙarshen tsarin raba makarantun ƙananan sakandare (JSS) da manyan sakandare (SSS).
Za a dauki matakin ne bayan bayanan da aka samu sun nuna cewa sama da ɗalibai miliyan 20 sun daina karatu kafin kai wa matakin manyan sakandare.

Source: Getty Images
Yara miliyan 20 ba sa zuwa sakandare
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da Kwamitin Aiwatarwa da Sa Ido na Ma’aikatar Ilimi kan ayyukan hukumar UBEC, in ji rahoton This Day.
A cewar ministan, tsarin raba JSS da SSS, wanda ya tilasta wa matakan biyu samun shugabanni da wasu kayan aiki daban, bai cimma manufar da aka kafa shi ba.
Ya ce:
“Muna da yara miliyan 20 da suka daina karatu daga firamare zuwa JSS. Ina yaran suke? Mun kuma gano cewa muna da makarantun firamare na gwamnati kusan 80,000, amma JSS kusan 15,000 ne kawai. Wannan bambanci ne na daya zuwa takwas.”
Karancin JSS ya jawo cunkoso
Alausa ya bayyana cewa rashin daidaiton yawan makarantun firamare da na JSS ya haifar da cunkoso a ƙananan sakandare, yayin da wasu manyan sakandare ke amfani da ƙarancin ɗalibai.
Ya ambaci wasu jihohin Arewa ciki har da Kaduna a matsayin misalai inda matsalar ta fi bayyana.
Ya ce:
“Wannan tsarin ya gaza. Za mu kawo ƙarshensa a hankali. Ba za mu ci gaba da samar da mukamai kawai saboda muna son ƙirƙirar matsayin darakta ba, alhali muna cutar da tsarin iliminmu. Abin da muke nema shi ne abin da ya fi dacewa ga kowane yaro ɗan Najeriya.”
Za a gabatar da kudirin a majalisar ilimi
Ministan ya ce za a gabatar da shawarar soke tsarin a taron gaba na Majalisar Ilimi ta Ƙasa, domin samun amincewar sauya tsarin.
Jaridar Punch ta ruwaito ministan ya bayyana cewa manufar matakin ita ce faɗaɗa damar samun ilimi tare da inganta sakamakon karatun ɗalibai.

Source: Getty Images
A wajen taron, ministan ya ƙaddamar da wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Rashid Aderinoye domin kula da ayyukan makarantun da UBEC ta samar.
Makarantun sun haɗa da:
- Makarantun zamani masu amfani da fasaha (Smart Schools)
- Makarantun harsuna biyu (Bilingual Schools)
- Madadin makarantun ilimi (Alternative Schools)
An bai wa kwamitin alhakin tabbatar da kammala ayyukan, mika su ga gwamnatocin jihohi da kuma fara amfani da su wajen koyarwa.
Gwamnati ta kawo sabon tsarin ilimi
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin ta gabatar da tsarin karatun bai daya na shekaru 12, wanda zai kawo karshen tsarin karatun sakandare na JSS, SSS.
Ministan Ilimin NAjeriya, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa wannan tsarin zai rage yawan daliban da ke fita daga makaranta da inganta ilimi.
Gwamnatin tarayyar ta ce sabon tsarin zai kawo cigaba mai dorewa a fannin ilimi, wanda ake sa ran zai dace da bukatun duniya.
Asali: Legit.ng

