'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Cibiyar NIPSS, an Gwabza Fada da Jami'an Tsaro
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi yunkurin kutsawa cikin harabar cibiyar NIPSS da ke Karu a jihar Plateau
- Ko a kwanakin baya 'yan bindigan sun kai hari a cibiyar inda suka yi dauki ba dadi da jami'an tsaro wanda ya jawo asarar rayuka
- A sabon harin da 'yan bindigan suka kai, jami'am tsaro sun fito inda aka artabun da ya jawo aka fatattaki maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Plateau - Jami’an tsaro a cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa (NIPSS) da ke Kuru, a jihar Plateau, sun dakile wani harin 'yan bindiga.
Jami'an tsaron sun dakile wani sabon yunkuri na wasu da ake zargi 'yan bindiga ne masu dauke da makamai na fasa katangar cibiyar, inda suka kashe daya daga cikin maharan yayin musayar wuta.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta gano cewa da misalin karfe 11:00 na daren ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026 ne ‘yan bindigan suka yi yunkurin shiga cibiyar amma jami’an tsaro suka fatattake su.
An kai hari a cibiyar NIPSS
Jaridar The Punch ta ce cibiyar ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026 ta hannun shugaban sashen hulda da jama'a, Dr. Osime Samuel.
Ta ce maharan sun fuskanci jami'an tsaro a wata kakkarfar musayar wuta, amma an tilasta musu ja da baya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin gaggawa da kuma hadin gwiwa daga jami'an tsaro.
A cewar sanarwar, an kashe daya daga cikin maharan a lokacin artabun, yayin da aka ce wasu da dama sun tsere da raunuka daban-daban.
Jami'an tsaro sun fatattaki 'yan bindiga
Sai dai, NIPSS ta ce maharan sun gaza ratsa katangar, inda ta jaddada cewa daukacin daliban da ke daukar kwasa-kwasai, ma'aikata, mazauna da kuma kayayyakin more rayuwa ba su samu wata matsala ba.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
Cibiyar ta kara da cewa hukumomin tsaro sun tsananta kokarin ganin sun gano tare da kamo wadanda ake zargin da suka tsere, yayin da aka karfafa sanya idanu da sauran matakan tsaro na rigakafi a ciki da kewayen cibiyar.

Source: Original
Yayin da take ba dalibai, ma'aikata, iyalansu da sauran jama'a kwarin gwiwa, NIPSS ta ce tsaron rayuka da dukiyoyi ya kasance babban abin da ta fi ba fifiko.
Haka kuma Cibiyar ta yaba da hanzari da kwarewa na hukumomin tsaro, sannan ta bukaci jama’a da su yi watsi da labaran karya da ka iya haifar da fargaba maras amfani.
Wannan lamari na baya-bayan nan ya zo ne kusan makwanni kadan bayan da wasu 'yan bindiga suka kai wa cibiyar hari da nufin shiga cikin harabar.
Mutanen gari sun yi artabu da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Dansarai da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina sun fuskanci turjiya daga mazauna yankin.
Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga kauyen ne a kan babura dauke da manyan makamai ciki har da bindigogin AK-47.
Wani mazaunin yankin ya ce mutanen garin sun yi nasarar fatattakar maharan, inda aka kashe ‘yan bindiga hudu yayin arangamar.
Asali: Legit.ng
