Gwamna da Ke Takarar Shugaban Kasa Ya Runtuma Kora, Ya Yi Sauye Sauye a Gwamnatin Oyo

Gwamna da Ke Takarar Shugaban Kasa Ya Runtuma Kora, Ya Yi Sauye Sauye a Gwamnatin Oyo

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sauke Kwamishiniyar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a, Toyin Balogun, tare da nada Faosat Sanni
  • Faosat Sanni ta taba rike wannan mukami daga 2019 zuwa 2023 kafin a sauya mata ma’aikata, amma yanzu ta dawo gidanta na farko
  • Gwamnan ya ce sauyin na cikin karamin gyaran majalisar zartarwar jihar, inda ya bukaci sababbin wadanda aka nada su yi aiki tukuru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya sauke kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar, Toyin Balogun, daga mukaminta, tare da nada Faosat Sanni a matsayin sabuwar kwamishiniya.

Sanarwar sauyin ta fito ne daga mai bai wa gwamna shawara kan harkokin kafafen yada labarai, Sulaimon Olanrewaju, a Ibadan, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta mamaye yankunan Legas, hanyoyi sun yi makil, lantarki ta katse

Gwamna Seyi Makinde ya yi karamin garambawul a majalisar zartarwar jihar Oyo
Gwamna Seyi Makinde, gwamnan jihar Oyo kuma dan takarar shugaban kasa. Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Makinde ya yi sauye sauye a gwamnatinsa

A cikin sanarwar, Olanrewaju ya ce Gwamna Makinde ya amince da wani karamin sauyi a majalisar zartarwar jihar wanda ya shafi sauya wurin aiki ga wasu jami’ai, in ji rahoton Punch.

Olanrewaju ya ce:

“Gwamna ya amince da karamin garambawul a majalisar zartarwa, wanda ya kai ga mayar da Faosat Sanni zuwa Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a. Sanni ta maye gurbin Toyin Balogun wadda aka sauke daga mukaminta.”

Gwamna Makinde ya gode wa Toyin Balogun bisa gudunmawar da ta bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi mata fatan alheri a ayyukan gaba.

Sauran nade-naden da Makinde ya yi

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Faosat Sanni ta taba zama kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar Oyo daga shekarar 2019 zuwa 2023.

A shekarar 2023, an sauya mata wurin aiki zuwa ma’aikatar ayyuka na musamman, kafin daga baya a sake tura ta ma’aikatar kasuwanci, masana’antu, zuba jari da hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Haka kuma, Gwamna Makinde ya nada wasu jami’ai a muhimman mukamai, ciki har da:

  • Ifeoluwa Akande — Shugabar kwamitin inganta filin jirgin sama na Samuel Ladoke Akintola
  • Isola Adekunle — Mai ba da shawara kan harkokin cikin gida na jam’iyya
  • Oladejo Oladokun — Mamba na wucin gadi a hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi

Sannan gwamnan ya aika sunan Olabode Ladipo, Sakataren Dindindin mai kula da Babban Gudanarwa, zuwa Majalisar Dokokin jihar domin tantance shi a matsayin kwamishina.

An umurci wadanda aka nada su yi aiki da sadaukarwa

A cewar sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Gwamnan, Segun Ogunwuyi, ya sanya hannu, nade-naden sun fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026.

Gwamna Makinde ya taya wadanda aka nada murna tare da bukatar su gudanar da ayyukansu da sadaukarwa, biyayya da jajircewa.

Wannan na zuwa ne bayan wani sauyin majalisar ministoci da gwamnan ya yi a watan Janairun 2026, inda ya sauke Sakataren Gwamnatin Jihar, Olanike Adeyemo, tare da nada Musibau Babatunde a matsayin sabon SSG.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com