Tashin Hankali: An Kashe Wani Magidanci saboda Yana Shirin Kara Aure a Jihar Kano

Tashin Hankali: An Kashe Wani Magidanci saboda Yana Shirin Kara Aure a Jihar Kano

  • Rahotanni sun nuna cewa an kama wata matar aure, Bilkisu Sani a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano kan zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu
  • An ruwaito cewa marigayin na shirin kara auren wata mata a matsayin matarsa ta biyu, wanda hakan ya fusata uwargidansa
  • Ma’auratan sun shafe kusan shekaru bakwai da aure kuma suna da ‘ya’ya biyu kafin aukuwar wannan mummunan lamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa wata matar aure mai suna, Bikisu Sani ta kashe mijinta, Hafizu Gausu saboda yana shirin kara aure.

Bayanai sun nuna cewa wannan lamari ya auku ne a yankin karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, kuma tuni aka kama matar bisa zargin kashe mijinta.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda aka kashe magidanci a Kano

Wani mazaunin yankin, Auwal Kazagi Rogo, ya shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a jiybJuma’a da misalin karfe 7:00 na yamma a yankin Katsalle da ke garin Rogo.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: An tura fitacciyar yar TikTok gidan yari kan 'zagin' wani ɗan siyasa a Kano

Ya ce mazauna yankin sun garzaya wurin bayan sun ji ihun matar Hafizu, wadda ta yi ikirarin cewa an yanka mijinta.

Kazagi ya ce:

“Da muka isa wurin, sai muka ga cewa ba a yanka shi ba, an buga masa wani abu a kai ne. Ya fadi cikin jini kuma ya mutu. Har ma an ga alamar cizo a kunnensa.”

Ya kara da cewa nan take aka kira ‘yan sanda, inda daga bisani suka kwashe gawar domin gudanar da bincike.

Hafizu na shirin kara aure

Kazagi ya kara da cewa ana zargin Hafizu Gausu ya kulla alaka da wata mata a baya-bayan nan, tare da shirin aurenta a matsayin matarsa ta biyu.

Ya ce wannan shawara ta jawo yawan sabani tsakanin sa da Bilkisu, wadda ake zargin ta yi alkawarin hana auren. Dattawan yankin sun taba shiga tsakani domin sasanta rikicin, amma rashin jituwa ya ci gaba.

Kazagi ya ce tun daga lokacin ‘yan sanda suka kama Bilkisu a matsayin wadda ake zargi da aikata laifin, yayin da bincike ke ci gaba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin kasuwa ɗauke da makamai, rayukan bayin Allah sun salwanta

An yi jana’izar Marigayi Hafizu

An binne mijin a safiyar yau Asabar a garin Rogo bisa tsarin da addinin Musulunci ya tanada.

Ma’auratan sun shafe kusan shekaru bakwai da aure, inda suka samu ‘ya’ya biyu. An kuma ce Bilkisu na dauke da cikin marigayin a halin yanzu.

Majiyoyi a yankin sun ce Hafizu Gausu har ya bukaci iyalan amaryarsa da su sanya ranar aurensu da watanni biyu saboda kishi da adawar da matarsa ke yi da auren.

Mata ta yi yunkurin kashe mijinta

Kun ji cewa wata matar aure yar kimanin shekara 23, Sadiya Lawal ta yi yunkurin kashe mijinta ta hanyar yanka masa wuya yana cikin barci a jihar Katsina.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Rundunar ta ce matar na tsare a hannunta yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262