Zaben 2027: Jihohin da Tinubu, Atiku da Peter Obi Ke Hasashen Samun Nasara
- Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi na neman faɗaɗa tasirinsu fiye da abin da suka samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
- APC ta ce tana da ƙarin ƙarfin siyasa bayan wasu gwamnoni sun sauya sheka, yayin da Atiku da Obi ke bayyana irin nasarorin da suke sa ran samu
- Kungiyoyin da ke goyon bayan Atiku da Obi sun yi ikirarin cewa sababbin tsare-tsare da haɗin gwiwa za su ƙara musu damar samun goyon baya a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, na ƙoƙarin faɗaɗa sansanonin siyasarsu fiye da abin da suka samu a 2023, yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara kusantowa.
Kowannensu na tafiya ne da wasu dabaru da tsare-tsaren siyasa daban-daban yayin da ake tunkarar zaben.

Source: Twitter
Legit Hausa ta fahimci cewa Tinubu zai tsaya takara ne ƙarƙashin tutar All Progressives Congress (APC), Atiku kuma ƙarƙashin African Democratic Congress (ADC), yayin da Obi zai tsaya ƙarƙashin Nigeria Democratic Congress (NDC).
Tinubu na neman ƙarin jihohi
A zaɓen 2023, Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726 a jihohi 12, ciki har da Rivers, Borno, Oyo da Jigawa.
Atiku ya zo na biyu da ƙuri’u 6,984,520, inda ya lashe jihohi 12 da suka haɗa da Kaduna, Katsina, Adamawa da Sokoto.
Obi kuwa ya samu ƙuri’u 6,101,533, inda ya lashe jihohi 11 da kuma Babban Birnin Tarayya, FCT. Daga cikin jihohin da Obi ya lashe akwai Enugu, Lagos, Anambra, Delta da Plateau.
A cewar wani rahoton Punch na Lahadi, 20 ga Satumban 2026, wani jami’in APC da ba a bayyana sunansa ba ya ce tsarin jam’iyyar ya fi ƙarfi yanzu fiye da shekaru biyu da suka gabata.
Jami’in ya danganta hakan da yawan sauya sheƙar gwamnoni zuwa APC mai mulki bayan sun fice daga jam'iyyunsu.

Kara karanta wannan
An farmaki magoya bayan Kwankwaso da Peter Obi a wurin gangamin siyasa, bidiyo ya fito
Gwamnoni sun koma APC
Gwamnoni tara da ke kan mulki, ciki har da Caleb Mutfwang na Plateau, Abba Kabir Yusuf na Kano, Sheriff Oborevwori na Delta, Peter Mbah na Enugu da Douye Diri na Bayelsa, sun koma APC daga jam’iyyun da suka kai su mulki a 2023.
Jami’in APC ya ce burin jam’iyyar shi ne samun nasara a akalla jihohi 20 na tarayyar Najeriya.
Ya kuma yi ikirarin cewa APC yanzu tana da kusan gwamnoni 31, idan aka kwatanta da kusan 22 a zagayen zaɓen da ya gabata.
Shugaban Ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga, ya ambaci Plateau, Nasarawa da Benue a matsayin wasu daga cikin jihohin da jam’iyyar ke fatan ƙara wa kan abin da ta samu a 2023.
Ya kuma ce a ganinsa Tinubu zai lashe dukkan jihohin Kudu maso Yamma shida, bayan ya samu nasara a huɗu kacal a 2023.
Atiku na hasashen samun ƙarin jihohi
A ɓangaren Atiku, tsohon shugaban ADC na kasa, Ralph Nwosu, ya yi nuni da wani zaɓen ra’ayi na cikin gida da ya ce yana nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai iya samun kashi 63 cikin 100 na ƙuri’un ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Tura ta kai bango: Dattawa daga Arewa sun aika sako ga Tinubu bayan fetur ya kai N1500
Nwosu ya kuma yi ikirarin cewa Atiku zai iya samun aƙalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a jihohi 28.
“Yanzu Atiku yana da tsarin siyasa mafi ƙarfi fiye da na 2023, kuma duk da cewa ya lashe jihohi 12 a wancan lokacin, zai lashe jihohi 28 a wannan karon,” in ji Nwosu.
Mataimakan Atiku kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe da Phrank Shaibu, ba su mayar da martani ga buƙatar jin ra’ayinsu kan wannan batu ba.
Ƙungiyar Obi na sa ran samun ƙarin tasiri
A ɓangaren NDC ma, masu goyon bayan Peter Obi sun bayyana kyakkyawan fata kan damar jam’iyyar a 2027.
Jagoran Obidient Movement na kasa, Yinusa Tanko, ya ce shigar tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, cikin haɗin gwiwar Obi ta faɗaɗa tasirin jam’iyyar a yankin Arewa.
“Ba mu da mutane irin su Kwankwaso a zaɓen da ya gabata, amma yanzu muna da shi,” in ji Tanko a ranar Alhamis, 17 ga Satumba.
Ya ƙara da cewa NDC na gabatar da ƙarin ’yan takara a zaɓen 2027, ciki har da wasu da ya bayyana a matsayin masu ƙarfi a jihohin Arewa. Tanko ya kuma ci gaba da cewa jam’iyyar na kan hanyar sake samun nasara a jihar Legas.

Source: Facebook
Obi ya ce a fitar da takardun karatunsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya nemi Jami’ar UNN da ke Nsukka ta fitar da bayanan karatunsa.
Peter Obi ya bukaci hakan ne bayan rahotannin daukar matakin shari’a da ke neman kwafin takardun karatunsa.
Asali: Legit.ng

