APC, ADC da Jam’iyyu 7 Sun Karɓi Lambar INEC, Za Su Shigar da Sunayen Ƴan Takara

APC, ADC da Jam’iyyu 7 Sun Karɓi Lambar INEC, Za Su Shigar da Sunayen Ƴan Takara

  • INEC ta ce jam’iyyun siyasa tara sun karɓi lambobin shiga domin shigar da bayanan ‘yan takarar shugaban kasa da ‘yan majalisa na 2027
  • Cikin jam’iyyun da suka karɓi lambar akwai APC, NDC, LP, ADC da wasu, yayin da har yanzu jam'iyyar PDP, NDC, APGA ba su karba ba
  • Hukumar ta bukaci jam’iyyun su guji jira har sai lokaci ya ƙure kafin su cike fom ɗin 'yan takara domin kauce wa matsalolin shigar da bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar INEC ta ce jam’iyyun siyasa tara da aka yi wa rajista sun karɓi lambobin shiga domin dora bayanan ‘yan takararsu na zaɓen shugaban kasa da majalisar tarayya na shekarar 2027.

Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zabe da hulɗa da jama’a, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu na iya kawo cikas ga shirin NDC na zaɓen 2027 a jihar Kano

INEC ta fara ba jam'iyyun siyasa lambar dora bayanan 'yan takarsu a shafinta
Dandazon magoya bayan APC (hagu), tutar LP (tsakiya) da dandazon 'yan PDP (dama). Hoto: @OfficialAPCNg, @NgLabour, @OfficialPDPNig
Source: UGC

Jam'iyyu 9 sun karbar lambar INEC

Jaridar Punch ta ruwaito Mohammed Haruna ya ce:

“Ya zuwa ƙarshen aikin ranar Litinin, jam’iyyun siyasa tara sun karɓi lambar shigar da bayanan 'yan takararsu domin tunkarar zaɓen kasa.”

A cewar Haruna, jam’iyyun da suka karɓi lambobin sun hada da:

  • Accord
  • AA
  • ADC
  • APC
  • LP
  • NDC
  • NDP
  • PRP
  • SDP

Yadda INEC ke ba jam'iyyu lambar

Kwamishinan ya bayyana cewa alhakin zuwa hukumar domin karɓar lambar shiga yana kan jam’iyyar da za ta shiga zaɓe, ba wai INEC ce za ta kai wa jam’iyyun lambobin a ofisoshinsu ba.

Ya ce duk wanda zai karɓi lambar a madadin wata jam’iyya, to dole ne ya gabatar da takardar izini daga shugabancin jam’iyyar, in ji rahoton The Nation.

Haruna ya ce hukumar ta fitar da ka’idojin gabatar da sunayen ‘yan takara, inda ya shawarci jam’iyyun siyasa su bi dokokin da aka gindaya.

Ya bayyana cewa tuni INEC ta horar da jami’an jam’iyyun kan yadda za su gudanar da aikin shigar da bayanan.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An daura sunan Atiku cikin 'yan takara a shafin INEC

INEC ta bukaci jam'iyyun siyasa su gaggauta dora bayanan 'yan takarsu ba sai lokaci ya kure ba
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan yana jagorantar wani taron hukumar a Abuja. Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Lokacin gabatar da fom ɗin takara

Kwamishinan ya ce INEC ta tsawaita lokacin rufe shigar da 'yan takara zuwa dare, domin bai wa jam’iyyun damar kammala aikin.

Ya ce idan wata jam’iyya ta jira har lokacin ya ƙure, to ba za a ɗora laifi kan INEC ba idan ta fuskanci matsala.

INEC ta tsara cewa daga ranar 27 ga Yuni zuwa 11 ga Yuli, jam’iyyun za su gabatar da fom ɗin ‘yan takarar shugaban kasa da na Majalisar Tarayya ta shafinta na musamman.

Haka kuma, gabatar da fom ɗin ‘yan takarar gwamna da na majalisun jihohi zai gudana daga 18 ga Yuli zuwa 8 ga Agusta, 2026.

INEC ta dauki bangare 1 a rikicin PDP

Tun da fari mun ruwaito cewa, INEC ta yi zama da shugabannin jam'iyyun siyasa a babban ofishinta na kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 5 ga watan Fabrairun 2026.

A taron, an ga wakilan tsagin PDP karkashin jagorancin Abdulraham Mohammed, wanda ke samun goyon baya daga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan ya jaddada cewa hukumar za ta yi biyayya ga hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com