Muhammad Malumfashi
21545 articles published since 15 Yun 2016
21545 articles published since 15 Yun 2016
Sakataren jam'iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ba zai koma jam'iyyar APC ba. Ya ce yana dan daram a ADC har sai sun kifar da APC.
Goodluck Jonathan ya yanke shawarar takarar shugaban kasa a 2027 a karkashin PDP, yayin da kungiyoyi ke rige-rigen kashe N100m don saya masa fom din takarar.
Amurka ta kwaso mutanenta 17 daga jirgin MV Hondius ranar 10 ga Mayu, 2026, inda aka samu mutum daya da kwayar cutar Hantavirus wadda ke da hadarin kisa sosai.
Gwamna Zulum ya ziyarci Bama ranar 11 ga Mayu, 2026, bayan guguwa ta kashe mutane 4 ta kuma rusa gidaje 1,200, inda ya ba kowane mamaci tallafin N500,000.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi martani ga zargin cewa jami'anta sun hallaka mutanen gari a garin bin yan bindiga a jihar Neja.
A labarin nan, za a ji cewa jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta bayyana zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kidime saboda kafuwarta gabanin 2027.
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa suna so su daina dogaro da Amurka game da karfin soja nan da shekara 10 masu zuwa.
Wata maniyyaciya daga Adamawa, Aishatu Muhammadu, ta rasu sakamakon ciwon zuciya a ranar 9 ga Mayu, 2026, yayin da take kan hanyar zuwa Madina a Saudi Arabiya.
A labarin nan, za a ji cewa kasashen Amurka da Iran sun sake samun rashin fahimta bayan bangarorin biyu sun ki amincewa da sharuddan sulhun da suka aika wa juna.
Muhammad Malumfashi
Samu kari