Rahoto: Hanyoyi 5 da Yakin Iran Ya Shafi yadda Mutane ke Samu da Kashe Kudi a Ingila
Ingila - Rikicin da aka dauki kwanaki fiye da 50 ana yi tsakanin Amurka, Isra'ila, da Iran ya girgiza tattalin arziƙin iyalai da dama a faɗin ƙasar Ingila.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wata cibiyar bincike ta yi hasashen cewa gidajen masu matsakaicin karfin na iya rasa makudan kudi a wannan shekarar sakamakon wannan yaƙi da aka tafka.

Source: Getty Images
Tasirin yakin Iran ga tattalin mutanen Ingila
Tsadar rayuwa na ƙaruwa yayin da farashin makamashi da sufuri ke tashi, wanda hakan ke shafar ikon sayayya na kowane ma'aikaci a ƙasar Ingila, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Wannan rahoto na musamman zai duba muhimman fannoni guda shida da wannan yaƙi ya shafa a cikin harkokin kuɗaɗen mutanen Ingila.
1. Farashin man fetur
Direbobi sun fuskanci tashin gwauron zabi na farashin mai a gidajen mai tun farkon fara wannan yaƙi tsakanin ɓangarorin uku

Kara karanta wannan
Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25
Ɗanyen mai shi ne babban sinadarin fetur da dizil, don haka tashin farashinsa a duniya ke sa cika tankin mota ya zamo abu mai wahala, saboda tsada.
Farashin fetur a Ingila ya kai kololuwa har zuwa 158.3p yayin da dizil ya kai 191.5p a lokacin da yaƙin ya yi zafi, kamar yadda rahoton MSN ya nuna.
Cika tankin mota ya ƙaru da fam 14, sannan cika mota mai amfani da dizal ya karu da fam 27 tun farkon rikicin na Iran.
2. Farashi mallaka da hayar gidaje
Kafin a fara wannan yaƙin, akwai tsammanin faɗuwar kudin ruwa na lamunin gidaje, amma rikicin ya jawo akasin haka ya faru a kasuwar gidaje ta Ingila.
Masu ba da lamuni sun ƙara farashi cikin sauri saboda fargabar cewa babban banki ba zai rage masu kudin ruwa ba, in ji rahoton Yahoo News.
Matsakaicin kudin ruwan na shekaru biyu ya tashi daga 4.83% a farkon Maris zuwa 5.78% a halin yanzu da ake ciki.
Bankin Ingila ya yi hasashen ƙarin kusan fam 80 a kowane wata ga masu sabunta yarjejeniyar lamunin gidajensu nan gaba.
3. Kuɗin makamashi
Akwai hukumar Ofgem da ke kare farashin wutar lantarki da iskar gas, amma wannan kariya tana da iyakar lokaci ga gidaje a Ingila

Source: Getty Images
Hasashe na nuna cewa kowane gida zai iya biyan fam 1,850 a shekara, maimakon fam 1,641 da ake biya a halin yanzu, duk da kokarin Ofgem.
Idan har yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe, aka dawo yaki, to ana sa ran samun gagarumin ƙarin kuɗin makamashi ga miliyoyin mutane a bazara.
Rahoton Commons Library ya nuna cewa gwamnatin Ingila na iya bayar da tallafi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi idan tsadar ta ci gaba har zuwa lokacin sanyi.
4. Tashin gwauron zabin tsadar rayuwa
Hasashen Bankin Ingila na cewa za a samu hauhawar farashin kayayyaki da 2% ya karu sosai sakamakon hare-haren da aka kai wa ƙasar Iran a watannin baya-bayan nan.
Masana sun yi imanin cewa saurin tashin farashin kayayyaki yana ƙaruwa kodayake ba zai kai matakin shekarar 2022 ba.
Cibiyar Resolution Foundation ta ce gidaje masu matsakaicin karfi za su iya rasa fam 480 a wannan shekarar saboda tsadar makamashi da abinci.
5. Kudin ruwa na iya karuwa
A tashin farko, Bankin Ingila ya dakatar da shirin rage kudin ruwa na 3.75% sakamakon fargabar hauhawar tattalin arziki da yaƙin Iran ya haifar.

Source: Getty Images
Rikicin ya sa mutane tsoron kashe kuɗi, wanda hakan na iya shafar cigaban tattalin arziƙin ƙasar baki ɗaya nan gaba.
Kwamitin da bankin ya kafa ya yi zama har sau biyu, kuma ya ayyana cewa kudin ruwa zai tsaya a 3.75%, kuma hakan zai iya karuwa idan aka gagara kawo karshen yakin.
Tarihin da Iran ta kafa a yaki da Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, kasar Iran ta shiga tarihin duniya bayan katse intanet na kwanaki 57 ba tare da tsayawa ba yayin da ake ci gaba da yaki.
Katsewar ta fara ne bayan hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila a Tehran, lamarin da ya keɓe ‘yan ƙasar daga duniya.
Duk da matsin lamba da rikicin diflomasiyya da Amurka, Iran ta ƙi shiga tattaunawa kai tsaye, yayin da ake ci gaba da takaddama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

