Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Mataimakin Gwamna a Jihar Sakkwato

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Mataimakin Gwamna a Jihar Sakkwato

  • 'Yan bindiga sun shiga yankin da mataimakin gwamnan jihar Sakkwato ya fito, sun yi awon gaba da mutane takwas jiya Alhamis
  • Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wadanda suka fada hannun maharan har da 'yan uwan mataimakin gwamnan
  • Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta kawo masu dauki don ceto su daga matsalar tsaron da suke fama da ita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Wasu ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da mutane takwas a kauyen Garin Idi da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka fada hannun 'yan bindigar suna da alaka da mataimakin gwamnan jihar ta Sakkwato, Idris Mohammed Gobir.

Taswirar Sokoto.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda harin ya faru a Sokoto

Kara karanta wannan

Tsaro: Kasar Jamus ta shigo Najeriya, ta shiga kauyukan da aka kai hare hare

Majiyoyi sun shaidawa Daily Trust cewa maharan dauke da mugayen bindigogi sun kai harin ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Alhamis.

Daga isarsu garin, 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, wanda ya tilasta mazauna kauyen tserewa zuwa daji domin tsira da rayukansu.

An ce ’yan bindigar sun shafe kusan awa biyu suna cin karensu babu babbaka a kauyen ba tare da wani daukin jami’an tsaro ba.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Ban taba jin harbin bindiga mai tsanani irin na jiya ba. Yanzu idan sun zo muna tsoro, amma idan sun tafi sai mu samu sauki saboda mun saba da hakan."

An sace yan uwan mataimakin gwamna

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce maharan sun zo ne a kan babura kusan takwas, inda suka tattara mutane kusan 30, galibi mata da yara, kafin daga bisani su saki wasu su tafi da mutane takwas.

Ta ce daga cikin wadanda aka sace, uku maza ne, biyar kuma mata ne, amma majiyar ta kara da cewa maharn sun saki wasu yara da wasu mutane saboda rashin isasshen wuri a kan baburan su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mutane sun tsere daga garuruwan Zamfara saboda wani matakin soja

An ce yawancin wadanda yan bindigar suka tafi da su zuwa cikin daji, ’yan uwan mataimakin gwamnan ne, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Mutane sun aika sako ga gwamnati

Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati, musamman mataimakin gwamna, da ya dauki matakin gaggawa domin magance matsalar tsaro da ke addabar yankin.

Wani mazaunin garin ya ce:

"Muna rokon sa ya dubi halin da muke ciki. A matsayin dansu kuma mataimakin gwamna, abin takaici ne yadda ake barin mu cikin wannan hali duk da kasancewarmu ’yan uwansa.”
Gobir.
Mataimakin gwamnan Sakkwato, Idris Mohammed Gobir a taron yaye dalibai da ya halarta a jami'ar jihar Nasarawa Hoto: Idris Mohammed Gobir
Source: Facebook

Sun nuna damuwa cewa duk da alakar da suke da ita da mataimakin gwamna, har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare a yankin ba tare da daukar matakin gaggawa ba.

Yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Yan bindiga sun sace bayin Allah a Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Achida da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka malamin addini da iyalansa a Plateau

Bayanai daga yankin sun nuna cewa maharan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da aƙalla mutane 25 a yayin harin.

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun fara farmakar wurin jami'an sa-kai ne da ke gefan garin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262