Jama'a Sun Tsallake Rijiya da Baya da 'Yan Ta'adda Suka Shuka Bam a Zamfara

Jama'a Sun Tsallake Rijiya da Baya da 'Yan Ta'adda Suka Shuka Bam a Zamfara

  • Rundunar ’yan sandan Zamfara ta ce ta dakile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Zurmi bayan samun rahoton barazanar tsaro
  • An kuma gano wani abin fashewa da ake zargin na’urar fashewa ce da aka binne a hanyar Gusau zuwa Gwashi da aka dasa don kashe jama'a
  • Rundunar ta ce babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni a hare-haren, tare da kammala aikin share hanyar domin tabbatar da tsaron matafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun dakile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar, bayan samun rahoton wata barazanar tsaro a yankin.

Rundunar ta kuma ce jami’anta sun gano tare da share wata na’urar fashewa da ake zargin an binne ta a kan hanyar Gusau zuwa Gwashi, a ƙaramar hukumar Bukuyum.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shan amarci, amarya ta saka guba a abincin ango

Sojoji sun hana tashin bam a Zamfara
Sufeto Janar na yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

AIT ta kawo labarin cewa cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar a ranar 12 ga Agusta, rundunar ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:00 na safe bayan samun rahoton barazanar tsaro.

Yan sanda sun kai dauki Zamfara

TVC News ta wallafa cewa sanarwar ta ce DPO na Zurmi ya gaggauta tura jami’an ’yan sanda domin ba da kariya ga al’ummar yankin da ke gudanar da aikin dasa bishiyoyi.

Sai dai, yayin da jami’an ke gudanar da aikin tsaro, wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai musu hari tare da buɗe wuta.

Jami’an tsaron sun samu mafaka sannan suka mayar da martani mai ƙarfi, inda suka yi musayar wuta da maharan tare da tilasta musu tserewa zuwa wani daji da ke kusa, kuma babu wani jami’in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa ko ya samu rauni a harin

Yan sanda sun share hanyar Zamfara

Kara karanta wannan

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Jariri sabon haihuwa da aka sace ya kubuta

A wani lamarin daban da ya faru da misalin ƙarfe 9:30 na safe a ranar, rundunar ta ce wata na’urar fashewa da ake zargin ’yan bindiga ne suka binne ta ta tashi a kan hanyar Gusau zuwa Gwashi.

An yi nasarar dakile harin Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayan samun rahoton lamarin, rundunar ta tura tawagar kwararru kan abubuwan fashewa, EOD, tare da haɗin gwiwar Sashen Dakile Laifuka na rundunar zuwa wurin.

Jami’an sun gudanar da cikakken bincike da share yankin, inda daga bisani aka tabbatar da cewa wurin ya kasance cikin aminci ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

Rundunar ’yan sandan ta buƙaci mazauna jihar da masu ababen hawa su ci gaba da taka-tsantsan tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi ko abin da suke zargi ga hukumomin tsaro.

Sojoji sun ragargaza yan bindiga

A baya, kun samu labarin cewa zaratan dakarun sojoji Najeriya sun kara zafafa ayyukan yaki da ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a Katsina da Zamfara a Arewacin Najeriya.

Rundunar sojin ta ce an kai samame ta kasa da sama kan yan bindiga a maboyarsu a karkashin Operation CLEAN SWEEP IV a yakunan da ke fama da matsalolin yan bindiga da ta'addanci.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa hare-haren sun tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe wasu daga cikinsu yayin da ake kwace makamai da ruguza maboyarsu a jihohin biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng