An Cafke Uwa da 'Ya'yanta cikin Masu Garkuwa da Mutane a Kaduna
- Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta cafke mutum shida da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Ikara
- An cafke mutanen ne bayan wani da ya tsere daga hannun masu garkuwa ya bai wa ‘yan sanda bayanan inda aka tsare shi a wani gida
- Rundunar ta ce an kai samamen gidan ne tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai, inda aka cafke waɗanda ake zargin tare da ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce ta cafke mutum shida da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Ikara ta jihar.
Rundunar ta bayyana cewa samamen ya faru ne a ranar Talata, 11 ga Agusta, 2026, bayan samun sahihin bayani daga wani wanda ya tsere daga hannun masu garkuwa da shi.

Source: Original
A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya wallafa a Facebook, wanda ya tsere ya bayyana wa ‘yan sanda gidan da aka tsare shi.
An cafke waɗanda ake zargi
Wanda ya tsere ya ce an tsare shi a gidan wani mai suna Ja’e Samalu, mai shekaru 65, da ke ƙauyen Dogon Pako a Ƙaramar Hukumar Ikara.
Bayan samun bayanan, Jami’in ‘Yan Sandan da ke kula da Ikara ya tattara jami’an rundunar tare da ‘yan kungiyar sa-kai domin kai samame gidan.
Sunayen mutanen da aka kama
A yayin samamen, an cafke Ja’e Samalu mai shekaru 65, da Abdul-Aziz Musa, wanda ake wa laƙabi da “Kire”, mai shekaru 35.
Sauran waɗanda aka cafke sun haɗa da Jafar Isah mai shekaru 25, Yunusa Musa mai shekaru 22, Shu’aibu Musa mai shekaru 20 da Rakiya Samalu mai shekaru 50.
Rundunar ta ce ana zargin Rakiya Samalu da kasancewa mahaifiyar wasu daga cikin waɗanda ake zargin, tare da kula da wanda aka tsare a gidan.
'Yan sanda na yin bincike
Rundunar ta ce dukkan waɗanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano irin rawar da kowannensu ya taka.
Haka kuma, rundunar ta ce za ta yi ƙoƙarin cafke sauran mambobin ƙungiyar masu garkuwa da ake zargi da hannu a lamarin.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Muhammad Rabiu, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin tare da mutanen da suka bayar da bayanan da suka taimaka wajen samun nasarar samamen.

Source: Twitter
Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da sanya ido tare da sanar da jami’an tsaro duk wani mutum, motsi ko abin da suke zargi a cikin al’ummominsu.
Kwamishinan ya kuma gargadi jama’a da su kula da masu aikata laifuffuka da ke amfani da gidajen zama a matsayin wuraren ɓoyewa ko tsare waɗanda aka yi garkuwa da su.
Rundunonin soji 4 za su fara aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya na shirin fara aiki da sababbin rundunonin soja guda huɗu da aka ƙirƙira domin faɗaɗa ƙarfin sojin wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.
Sabbin rundunonin na daga cikin shirin sake fasalin rundunar sojin Najeriya, bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙara yawan rundunonin daga takwas zuwa 12.
Sabon tsarin na da nufin rarraba tsarin jagoranci da kula da ayyukan soji, tare da inganta saurin mayar da martani kan hare-haren ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.
Asali: Legit.ng


