Dogo Gide: Sojoji Sun Samu Nasarar Cafke Na Kusa da Jagoran 'Yan Ta'adda da Wasu Miyagu 60
- Sojojin Najeriya sun kama wani jami’in ISWAP da ake zargi yana aiki tare da shugaban ’yan ta’adda Dogo Gide
- An kuma kama wasu mutane 60 da ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda a jihar Adamawa yayin aikin da sojoji suka gudanar
- Sojoji sun cafke wasu ’yan ta’adda biyar tare da lalata sansanoninsu a Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dakarun Sojojin Najeriya sun kama wani fitaccen jami’in ’yan ta’adda da ake alaƙanta shi da shugaban ’yan ta’adda Dogo Gide.
Sojojin sun kuma cafke wasu mutane 60 da ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda a wasu hare-hare daban-daban.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce rahoton soji da aka fitar a ranar Alhamis, 14 ga Agustan 2026 a Abuja, ya ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin 12 da 13 ga Agusta.
An kama jami’in Dogo Gide
A Kaduna, sojojin Bataliyar 4 Demonstration sun kama wani da ake zargi jami’in ISWAP ne kuma yana aiki tare da shugaban ’yan ta’adda Dogo Gide.
Sojojin sun ce sun tare wanda ake zargin ne a shingen binciken ababen hawa na Kadage, yayin da yake safarar kayan sojan da na ƙasashen waje guda bakwai da aka ɗinka zuwa wani sansanin ’yan ta’adda.
An ƙara da cewa binciken farko da aka yi wa wanda ake zargin ya nuna cewa shi na kusa da Dogo Gide ne kuma yana kai masa kayan tallafin da ake buƙata.
An kama mutane 60 a Adamawa
Haka kuma, sojojin Bataliyar 226 tare da haɗin gwiwar mafarauta sun kai samame wata tashar mota da ke yankin Gombi a Adamawa, Tribune ta kawo labarin.
An gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargi da haɗin gwiwa da ’yan ta’adda, waɗanda ake zargi suna ɓoye kansu a matsayin ’yan kwadago da masu talla.
Sojojin sun ce aikin ya kai ga kama mutane 60 da ake tsare da su a yanzu domin ci gaba da bincike.
Sojoji sun kwato bam a Zamfara
A Zamfara, sojojin Birged na 1 sun kwato wani bam na RPG yayin da suke sintirin yaƙi a kusa da Tunga-Jambako, a ƙaramar hukumar Maradun.
A halin da ake ciki, sojojin Operation WHIRL STROKE sun kama wasu mutane biyar da ake zargi ’yan ta’adda ne yayin hare-haren ƙarfi kan sansanonin ’yan ta’adda da ake zargi da ke Chito, Jootar da Ikyior a ƙaramar hukumar Ukum ta Benue.
Sojojin sun kuma lalata sansanonin tare da kwato babura biyu, bindigogi biyu da aka ƙera a gida da wasu kayayyaki.

Source: Twitter
Sojoji sun zafafa hare-hare kan 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kara zafafa kai hare-hare yaki kan ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu dauke da makamai a jihohin Katsina da Zamfara.
Dakarun sun kai hare-hare ta sama da kasa kan yan bindiga a wadannan jihohi a karkashin Operation CLEAN SWEEP IV, wani sabon mataki na Operation Fansan Yamma.
Asali: Legit.ng

