Rikicin PDP: Matakin da Kwamitin Amintattu Ya Dauka bayan Hukuncin Kotun Koli
- Kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP da ke tsagin Tanimu Turaki SAN ya ɗauki matakin gaggawa bayan hukuncin kotun koli
- A ranar 30 ga watan Afrilu na shekarar 2026 ne kotun koli ta sabule Tanimu Turaki daga jagorancin jam'iyyar PDP ta kasa
- Kwamitin amintattu (BoT) ƙarƙashin Adolphus Wabara dauki mataki domin rufe gibin shugabanci a jam'iyyar ta PDP
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara, ya sanar da karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar bayan hukuncin kotun koli.
A ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu na shekarar 2026 ne kotun kolin Najeriya ta soke sahihancin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na ɓangaren Kabiru Turaki.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa Wabara ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan mataki ya dace da kundin tsarin mulkin PDP domin kauce wa gibin shugabanci a matakin ƙasa.
An kama ragamar PDP
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Wabara ya ce an ɗauki wannan mataki domin ci gaba da tabbatar da gudanar da PDP na tare da matsalar shugabanci ba.
Kotun ƙolin ta yanke hukunci ne da rinjaye Alkalai 3-2, inda ta amince da hukuncin kotunan baya da suka soke taron Ibadan da ya samar da ɓangaren Tanimu Turaki SAN.
Mai shari’a Stephen Adah ya bayyana cewa an gudanar da taron ne sabanin umarnin kotu, lamarin da ya sa aka watsar da ƙarar da aka shigar.
Sai dai wasu alkalai biyu sun yi sabanin ra’ayi, suna cewa rikicin cikin gida ne na jam’iyya ba wanda ya kamata a kawo waje ba.
Hukuncin kotu ya karfafa wa ɓangaren Wike
Duk da haka, hukuncin ya ƙarfafa ɓangaren da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya riga ya gudanar da nasa taron a watan Maris na shekarar 2026.
Ya ce duk wani mataki da suka ɗauka, daga ciki har da naɗin Abdulrahman Mohammed a matsayin mukaddashin shugaba da tashin Samuel Anyawu ke yi ya saba doka.

Source: Facebook
Ya ce hukuncin kotun ya kara tabbatar da haramcin jagorancin Sanata Samuel Anyanwu, Umar Bature, da Kamaldeen Ajibade wanda shi ma ya kore su daga mukamansu.
Sanarwar ta ce:
“Yayin da kotun koli ta soke taron Ibadan, haka kuma a cikin hukuncin alkalan kotun guda biyar ya dakatar da Sanata Samuel Anyanwu, Hon. Umar Bature, da Kamaldeen Ajibade daga mukamansu na sakataren kasa, sakataren ysare-tsare na lasa, da lauyan jam’iyyar."
“Ma’anar hukuncin da kotun koli ta yanke shi ne duk wasu matakan da Sanata Samuel Anyanwu, Hon. Umar Bature, da Barr. Kamaldeen Ajibade suka dauka, ciki har da nada Abdulrahman Mohammed a matsayin mukaddashin Shugaban Kasa, kafa Kwamitin Rikon Kwarya na Kasa, da kuma gudanarwa da sakamakon taron jam’iyyar na ranar 29 ga Maris, 2026 a Abuja, duk ba su da inganci a doka, sun zama a banza."
Kotu ta yi hukunci kan rikicin PDP
A baya, mun wallafa cewa kotun koli ta raba gardama game da shari'ar da ake yi tsakanin ƴaƴan jam'iyyar PDP wanda ya kawo rigima mai tsanani a Najeriya.
A ranar is 30 ga watan Afrilun 2026, kotun ta yi watsi da karar daukaka kara da tsagin PDP karkashin jagorancin Taminu Turaki ya shigar gaban kotun.
lkalin kotun koli, Mai shari’a Stephen, ya ce taron PDP da aka gudanar a Ibadan ya saba wa hukuncin baya na babbar kotun tarayya, saboda ta soke shi baki daya.
Asali: Legit.ng


