A gaban Mai Mala Buni: Gwamnan Katsina Ya Kaddamar da Titi Mai Nisan Kilomita 39

A gaban Mai Mala Buni: Gwamnan Katsina Ya Kaddamar da Titi Mai Nisan Kilomita 39

  • Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da titin Ingawa–Dutsi–Shargalle mai tsawon kilomita 39 da aka kammala
  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya halarci taron a matsayin babban baƙo na musamman domin ƙaddamar da wannan gagarumin aikin
  • Da yake jawabi ga mahalarta taron, Gwamna Dikko Radda ya bayyana yadda titin zai share hawaye ga manoma, da bunkasa tattalin arziki

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina – Gwamna Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da gagarumin aikin gina hanyar Ingawa zuwa Dutsi zuwa Shargalle a ranar 1 ga watan Mayun 2026.

Aikin gina titin mai tsawon kilomita 39, wani ɓangare ne na ƙudurin gwamnatin Radda na sabunta muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar Katsina.

Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da titin Dutsi zuwa Shargalle a Katsina
Gwamna Dikko Radda ya na daga hannu ga mahalarta taron kaddamar da titin Dutsi zuwa Shargalle. Hoto: @dikko_radda
Source: Twitter

Radda ya kaddamar da titin Ingawa-Shargalle

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai girma Gwamna Dikko Radda ya fitar da hannunsa a shafinsa na X, inda ya yi bayani game da tasirin aikin ga jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

A sanarwar da ya fitar, wadda ta kunshi jawabin ƙaddamar da hanyar, Radda ya bayyana cewa wannan titi zai taka rawa sosai wajen inganta harkokin noma, kasuwanci, da kuma sauƙaƙa samun ayyukan kiwon lafiya da ilimi ga al'ummar yankin.

"A yau mun hadu a karamar hukumar Ingawa, inda muka kaddamar da titin Shargalle zuwa Ingawa, mai nisan kilomita 39.
"Na yi farin ciki da ya zamana cewa na kaddamar da wannan gagarumin aiki a gaban d'an uwana, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, wanda ya halarci taron a matsayin bako na musamman.
"Wannan hanya za ta zamo dami a kala ga manoma, 'yan kasuwa da al'ummar Shargalle, Dutsi da Ingawa.

- Gwamna Dikko Umaru Radda.

Tarihin titin da tasirinsa ga al'umma

Gwamna Radda ya tunatar da cewa wannan titi yana da tarihi mai tsawo, inda aka fara gina shi a lokacin tsohon Gwamnan jihar Kaduna, marigayi Balarabe Musa.

Bayan haka, marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya sake gyara shi a lokacin yana gwamnan jihar Katsina. Gwamnan ya ce gwamnatinsa na ci gaba da gina wannan tarihi ne domin dacewa da buƙatun yau da kullum.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kashe Naira tiriliyan 1.1 a Kaduna, Uba Sani ya yi bayani

Gwamna Dikko Radda ya ce titi mai nisan kilomita 39 da ya kaddamar a Katsina zai bunkasa tattalin arziki
Gwamna Dikko Umaru Radda ya na jawabi a wajen kaddamar da titin Shargalle zuwa Ingawa. Hoto: @dikko_radda
Source: Twitter

A wata sanarwar MS Ingawa, babban mai tallafawa gwamnan Katsina ta fuskar dabaru da watsa labarai, kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya yi magana kan tasirin titin.

Sani Magaji Ingawa ya bayyana cewa titin zai rage lokacin tafiya, ya inganta tsaro, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin yankunan Ingawa, Dutsi, da Shargalle.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya jinjina wa takwaransa na Katsina duba da hangen nesa da ya nuna wajen samar da waɗannan ayyuka.

Karanta sanarwar Dikko Radda a kasa:

Dikko Radda ya lashe lambar yabo

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe lambar yabo ta gwamnan da ya fi kowane aiki a shekarar 2025.

Aso Multimedia ce ta ba gwamnan wannan lambar yabo domin yabawa kokarin da yake wajen kawo ci gaba da fannoni daban-daban a Katsina.

Kwamishinar harkokin mata ta Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta faɗi wasu daga cikin ayyukan da Dikko Raɗɗa ya yi a shekaru biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com