'Yan Najeriya Sun Rikita Amurka da Damfara, Sun Wawure Miliyoyin Daloli a Jihohi 47
- Alkalin kotun Amurka ya samu wani dan Najeriya da 'yan wasu kasashe da laifin damfara ta yanar gizo, inda suka wawure dala miliyan 215
- Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin shugaba Donald Trump ta bayyana cewa tana cigaba da yaki da aikata laifuffukan da ake ta intanet
- Yayin zaman kotun da aka yi, alkalin ya bayyana cewa bayan sun wawure makudan kudi daga mutane da dama sun tura su wani asusun banki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Wata kotu a Amurka ta samu dan Najeriya, Oluwafemi Michael Awoyemi da wasu abokan aikinsa biyu da laifi bisa rawar da suka taka a wata damfara ta yanar gizo da ta kai dala miliyan 215.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka damfara sun kai sama da mutane 1,000 a jihohi 47 na Amurka da kasashe 19 a fadin duniya.

Source: Getty Images
An bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ofishin lauyan gwamnatin Amurka na yankin Arewacin Ohio ya fitar ranar Alhamis, 30 ga Afrilun 2026 a kafar X.
Hukuncin da aka yi a kotun Amurka
Hukuncin ya biyo bayan shari’ar kwanaki hudu da aka gudanar a Toledo, Ohio, inda masu gabatar da kara suka bayyana yadda wata kungiyar masu satar bayanan imel da ke da alaka da Najeriya ta yi damfara.
A cewar masu gabatar da kara na Amurka, Awoyemi mai shekaru 40, tare da Aruan Drake mai shekaru 37 da Peter Reed mai shekaru 35 ake zargi.
An same su da laifin hada baki wajen damfarar kudi ta hanyar sadarwa, yayin da Awoyemi da Drake kuma aka same su da laifin hada baki wajen sace kudi.
Bayanin shaidu a kotun kasar Amurkar
Shaidu a kotu sun nuna cewa kungiyar tana cutar kamfanoni, kungiyoyi da mutane ta hanyar kutse cikin asusun imel, bibiyar bayanan sadarwa, da aika sakon biyan kudi na bogi suna nuna kamar na gaskiya ne.
An ce 'yan damfarar sun karkatar da manyan kudi zuwa asusun kamfanonin bogi, bayan haka aka sace ta hanyar kamfanonin karya, shaidar tura kudi na bogi da hanyoyin aika kudi ta bayan fage.

Source: Twitter
Karin bayani kan shari'ar
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa an sarrafa kusan dala miliyan 50 daga cikin kudin da aka sace ta wani wajen musayar kudi a yankin Chicago da wani wanda ake kara Lon Goodman ke gudanarwa.
Wadanda abin ya shafa suna jihohi masu muhimmanci na Amurka kamar Ohio, California, Texas, Florida da New York, da kuma kasashe irin su Canada, Jamus, Italiya, Australia da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Nairametrics ta wallafa cewa wani kamfani da aka damfara ya tura kusan dala miliyan 2.7 zuwa asusun wani kamfani na bogi da kungiyar 'yan damfarar ke iko da shi.
Batun sarkin da Amurka ta kama
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jihar Osun ta yi watsi da rahoton da ke cewa ta tsige Apetumodu na Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede da ke daure a Amurka.
Wannan na zuwa ne bayan wata jita-jita da ta yadu a kafafen sada zumunta ranar Litinin cewa an tsige Oba Oloyede daga mukaminsa.
An samu sarkin da laifin hadin baki domin cin gajiyar shirye-shiryen lamunin gaggawa na COVID-19 da aka kirkiro domin taimakawa kananan ‘yan kasuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

