Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za Ta Hukunta Jami'an da Suka Tsakure Albashin Ma'aikata
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin binciken zargin cire Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikatan Kano
- Ya bayyana haka a yayin da ya ke jinjina wa ma'aikata da suka zage suna aiki domin bunkasa tattalin arzikin jihar Kano
- Wannan na zuwa ne bayan Kwamishina yada labaransa, Ibrahim Waiya ya kama sunan tsohon jami'in gwamnati a badakalar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci sakataren gwamnatin Jiha (SSG), Umar Farouq Ibrahim, da ya kafa kwamiti domin binciken zargin cire Naira biliyan 1.5 daga albashin ma’aikatan gwamnati a lokacin tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Abdullahi Musa.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a 1 ga watan Mayu na yayin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026 da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan
Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Source: Facebook
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa wannan na zuwa bayan koke da shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) na jihar, Kwamared Kabir Inuwa ya gabatar da ya ce an kama sunan tsohon jami'in gwamnati a lamarin.
Gwamnan Kano ya daukar wa ma'aikata alkawari
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa ma’aikata cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin, za a hukunta shi.
Haka kuma ya ɗauki alƙawarin cewa za a tilasta wa duk wanda aka kama da hannu a cikin badakalar da ya mayar da kudin da aka zarge shi da karkatarwa.
Ya ce:
“Na umarci SSG da ya kafa kwamiti domin binciken zargin karkatar da Naira biliyan 1.5 da ake yi wa tsohon shugaban ma’aikata.”
Wannan mataki ya biyo bayan zargin da kungiyoyin kwadago suka yi cewa an cire wadannan kudi ba bisa ka’ida ba daga albashin ma’aikata, kuma kwamishinan yada labarai, Ibrahim Waiya ya yi zargin da hannun tsohon shugaban ma'aikata a lamarin.
Gwamnan Kano zai inganta rayuwar ma'aikata
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana, tare da kare hakkin ma’aikata a jihar Kano.

Source: Facebook
Yayin da yake jawabi ga ma’aikatan, gwamnan ya bayyana ma’aikata a matsayin ginshikin tafiyar da gwamnati da ci gaba, yana mai cewa lafiyar kwakwalwa, tabbacin aiki da albashi mai kyau na da matukar muhimmanci wajen kara ingancin aiki.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da fifita shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki, inganta tsaro da kuma habaka tattalin arziki domin rage talauci da magance kalubalen wuraren aiki.
Gwamnan ya bayyana cewa ya gaji bashin sama da Naira biliyan 48 na hakkokin ritaya da kudin mutuwa, inda ya ce an riga an biya Naira biliyan 32 daga ciki.
Ya kuma yi alkawarin kammala biyan sauran bashin kafin karewar wa’adin mulkinsa da ke tafe a nan gaba kaɗan.
Ya ce gwamnatinsa na biyan albashi a kan lokaci da kuma aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 71,000, wanda ya sanya Kano cikin jihohin farko da suka fara amfani da tsarin.
Gwamnan Kano ya daura kan ƴan siyasa
A baya, mun kawo labarin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya zargi wasu yan siyasa da amfani da matsalar tsaron Najeriya domin cimma burinsu.
Gwamna Abba Gida-Gida ya ce wasu mutane marasa kishin kasa ke rura matsalar tsaro, wanda hakan ke kawo cikas ga kokarin samar da tsaro a kasar nan.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tsare rayukan al'umma da ke rayuwa a dukkanin sassan jihar Kano.
Asali: Legit.ng

