Kasar Iran Ta Ta Canza Shawara kan Batun Sulhu da Amurka, Ta Mika Sabon Tayi
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara nuna alamun za a ci gaba da tattaunawar sulhu tsakaninta da Amurka don cimma matsaya ta karshe
- Bayanai sun nuna cewa Iran ta sake mika sabon tayi ga Amurka ta hannun mai shiga tsakani watau kasar Pakistan a daren jiya Alhamis
- Wani masani ya bayyana cewa da yiwuwar Amurka ta aminta da sabon tayin ko da kuwa ba ta samu abin da take so ba kan shirin nukiliyar Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tehran – Iran ta mika sabon tayi da tsarin tattaunawa ga Amurka ta hannun kasar da ke shiga tsakani watau Pakistan.
Rahotannin da ke shigowa sun ce an mika takardar da ke kunshe da sabon tayin Iran ne a daren ranar Alhamis, amma ba a bayyana cikakken abin da ta kunsa ba.

Kara karanta wannan
Iran ta karyata Amurka kan asarar da Trump ya yi a yaƙin Isra'ila, ta fadi adadin dalolin

Source: Getty Images
Yadda aka samu tsaiko a zaman Amurka-Iran
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa Iran da Amurka sun yi zagaye daya kacal na tattaunawa a lokacin da aka tsagaita wuta bayan kusan kwanaki 40 na yaki da ya barke a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Tun daga lokacin tattaunawar ta tsaya cik, musamman bayan Amurka ta kakaba takunkumin kulle tashoshin jiragen ruwa na Iran, yayin da ita kuma ta takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
An ce tun bayan fara yakin, Iran na barin kadan daga cikin jiragen ruwa su rika wucewa ne kawai, amma ba ta barin jiragen da ke da alaka da Amurka ko Isra'i'a.
Iran tana tattaunawa makwabtan kasashe
A ranar Juma’a, ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi tattaunawa ta waya da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Turkiyya, Iraki da Azerbaijan kan sababbin matakan da Iran ke dauka domin kawo karshen yakin.
Fadar White House ta Amurka ta ki yin tsokaci kan sabon tsyin, tana mai cewa ba za ta bayyana bayanan tattaunawar ta sirri ga jama'a ba.

Kara karanta wannan
Trump ya ki amince wa da wani bangare a sabon tayin sulhu da Iran ta yi wa Amurka
Mai magana da yawun White House, Anna Kelly, ta ce Shugaban kasa Donald Trump ya bayyana karara cewa Iran ba za ta taba mallakar makamin nukiliya ba, cewar rahoton Vanguard.

Source: Getty Images
Ra’ayoyin masana
Wani masani, Farfesa Sultan Barakat, ya ce akwai yiwuwar Amurka ta mayar da hankali kan sabon tayin na Iran, ko da kuwa bai mayar da hankali kai tsaye kan shirin nukiliya ba.
Ya kara da cewa wasu kalaman jami’an Amurka sun nuna cewa ba a ganin Iran na barazana kai tsaye da makamin nukiliya a halin yanzu, wanda zai iya bude kofar tattaunawa.
Haka kuma ya ce Iran ta nuna juriya duk da takunkumin da aka kakaba mata, inda ta guji kai hari ga jiragen ruwan Amurka tare da neman wasu hanyoyi na kasuwanci ta Pakistan da sauran wurare.
Amurka ta kashe $25bn a yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kashe kimanin Dala biliyan 25 a yakin da kasar ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron Amurka, Jules Hurst, ne ya tabbatar da hakan ga mambobin Majalisar Dokokin kasar.
A cewar Hurst, kuɗaɗen sun tafi ne wajen sayo manyan makamai, makaman kariya daga makamai masu linzami, da kuma tallafawa dakarun Amurka dake jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng