"Ni Masoyinsa ne": Davido Ya Faɗi Yadda Ya ke Musayar Sakonni da Ronaldo
- Fitaccen mawaki 'dan Najeriya, Davido ya ce shi babban masoyin Cristiano Ronaldo ne kuma su kan yi musayar sakonni lokaci zuwa lokaci
- Mawakin ya bayyana cewa ya goyi bayan Portugal a Gasar Kofin Duniya ta 2026 saboda yana da abokai a tawagar kasar da ya ke ji da su
- Davido ya nuna abin da ya ce hirarsa ce da Ronaldo, inda ya tabbatar wa magoya bayansa cewa ya na tare da fitaccen 'dan wasan kwallon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa shi babban masoyin fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo ne.
A yayin da ya ke tabbatar da hakan, ya kara da bayyana cewa shi da Ronaldo su kan yi magana akai-akai saboda abota da ke tsakaninsu.s

Source: Facebook
Davido ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da shahararren mai yada shirye-shiryen intanet, Carter Efe kuma aka wallafa shashensa a shafin Instabloq a X.
Ni masoyin Ronaldo ne - Davido
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa mawakin ya ce ya kasance yana goyon bayan kasar Portugal ta lashe Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 saboda yana da abokai da dama a cikin tawagar kasar.
A cewarsa:
"Saboda ina da abokai da yawa a tawagar Portugal. Ina son Portugal ta lashe gasar."
Lokacin da Carter Efe ya yi zargin cewa hakan na da nasaba da Cristiano Ronaldo, sai Davido ya amsa da cewa:
"Ina son Ronaldo, ni masoyinsa ne."
Davido ya nuna hirarsa da Ronald
Davido ya kara da cewa yana ci gaba da tattaunawa da Ronaldo, inda ya tabbatar da cewa hirarsu na tafiya ba tare da an samu tsaiko ba.
Domin tabbatar da ikirarinsa, mawakin ya nuna wa Carter Efe abin da ya bayyana a matsayin hirarsa da Ronaldo a wayarsa.

Source: Getty Images
Tun daga lokacin ne bidiyon ya fara yaduwa sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka rika tofa albarkacin bakinsu kan ikirarin na Davido.
Sai dai har zuwa yanzu, babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da cewa tattaunawar da Davido ya nuna da gaske tsakaninsa ce da Cristiano Ronaldo.
A baya ma, an sha ganin Davido tare da fitattun 'yan wasan kwallon kafa na duniya, kuma ya kan bayyana sha'awarsa ga wasan kwallon kafa.
Christiano Ronaldo zai angwance
A baya, kun ji cewa rahotanni sun ce fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo zai auri budurwarsa Georgina Rodriguez a mako mai zuwa a garinsu na Funchal da ke Portugal.
Ana sa ran za a daura auren a babban cocin Funchal kafin baki su wuce wani katafaren otal mai matukar girma domin liyafar bikin fitaccen dan kwallon kafan da ya shahara a duniya.
Ronaldo da Georgina sun kara janyo hankalin jama'a bayan da suka nuna zobban lu'ulu'unsu masu tsada gabanin bikin da ake sa ran za su yi bayan sun shafe shekaru tare da da yara a tsakani.
Asali: Legit.ng

