Fahad Dankabo: Matashi Zai Kara da Ɗan Majalisa Mai Ci a Kano, Ya Kai Takarda APC
- Hon. Fahad Dankabo ya ayyana neman takarar kujerar wakilin Gwarzo da Kabo a Majalisar Wakilai ta tarayya karkashin jam’iyyar APC
- Dankabo ya bayyana cewa ya yarda ya nemi takarar ne bayan matsin lamba daga al’umma da kuma shawarwarin jiga-jigan siyasarsa
- Dan takarar ya yi alkawarin karkata akalar wakilcin sa wajen inganta ilimi, tallafawa mata da matasa, da kuma samar da ababen more rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano – Hon. Fahad Dankabo ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta neman tikitin takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gwarzo da Kabo.
Dankabo ya bayyana cewa wannan mataki ya zo ne a matsayin amsa kiran da al’ummar yankin suka dade suna yi masa na ganin ya wakilce su a matakin tarayya.

Source: Facebook
Fahad Ɗankabo ya fito takarar majalisar wakilai
Aliyu Maiwake Garo, darakta janar na watsa labaran Hon. Fahad Dankabo ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Legit Hausa.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar tarayya ya rasa tikitin APC, an ba 'dan fitaccen attajiri a jihar Katsina
Aliyu Maiwake Garo, ya ce Dankabo ya jaddada wa magoya bayansa cewa ba zai nemi mulki don amfanin kansa ba, sai don hidimtawa al'ummar da za ta zabe shi.
Hon. Fahad Dankabo ya bayyana cewa yankin Gwarzo da Kabo na bukatar wakilci mai ma’ana wanda zai karbo masu hakkokinsu tare da gina makoma mai kyau ga matasa.
"Mun fara kai ziyara ofishin jam'iyyar APC na ƙananan hukumomin Gwarzo da Kabo, daga nan muka wuce ofishin jam'iyyar na jiha don kai tajardar nuna sha'awar tsaya wa takara ga shugaba, Umar Haruna Doguwa.
"Gaskiya mun ji dadin yadda aka tarbe mu, duk da shi ciyaman baya nan, sai sakataren jam'iyya, Farfesa Mohammed Sabo Bichi da sauran Exco muka tarar. Sun ba Hon Fahad Dankabo shawarwari tare da ƙarfafa masa gwiwa."
- Aliyu Maiwake Garo.
Kuduri da manufofin takarar Dankabo
Da yake magana ga magoya bayansa, Fahad Dankabo ya zayyana muhimman fannoni da zai mayar da hankali a kai muddin ya samu nasara, wadanda suka hada da:
- Samar da shirye-shiryen dogaro da kai domin rage radadin talauci ga matasa sa mata.
- Inganta cibiyoyin ilimi da fafutukar samar da kayan aiki ga asibitocin karkara.
- Tabbatar da cewa an gyara hanyoyi tare da samar da ruwan sha mai tsafta.

Kara karanta wannan
Sanata ya daina jayayya, ya bi bayan dan takarar gwamna da Zulum ya tsayar a Borno
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar APC da su hada kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar, inda ya gargadi magoya baya da su nisanci siyasar zagi ko rarrabuwar kai.

Source: Facebook
Shirye-shiryen shiga zabe
Rahotanni daga ofishin yakin neman zabensa sun tabbatar da cewa tuni aka kammala dukkan shirye-shiryen da suka shafi sayen fom din takara da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.
Darakta Janar na kafafen yada labaran Hon. Fahad ya kuma tabbatar da cewa an gabatar da takardar sha'awar, inda ya kara da cewa matakai na gaba sun hada da siyan fom ɗin tsayawa takara, in ji rahoton Guarantee Radio Kano.
A halin yanzu, Hon. Gwarzo Abdullahi Muazu (Baban Gandu) ne ke rike da wannan kujera, kuma an zabe shi a 2023 karkashin jam'iyyar APC.
Tsarin APC na zaben fitar da gwani
Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta sanar da fara sayar da fom ga duk masu sha'awar yin takara a zaben 2027 daga ranar 25 ga Afrilu, 2026.
Jam'iyyar ta fitar da jadawalin gudanar da zabukan fitar da gwani, inda za a gudanar da na shugaban kasa a ranar 23 ga Mayu, 2026.
APC za ta yi amfani da tsarin zaɓen kato-bayan-kato ko kuma sulhu, amma jam'iyyar ta fadi abin da zai faru idan matsala ta taso.
Asali: Legit.ng