An Tsaurara Matakan Tsaro a ofishin INEC yayin da Ake Shirin Zaben Gwamnan Osun

An Tsaurara Matakan Tsaro a ofishin INEC yayin da Ake Shirin Zaben Gwamnan Osun

  • Jami’an tsaro da dama sun mamaye ofishin hukumar zabe, INEC da ke kan hanyar Gbongan-Ibadan a Osogbo a jihar Osun
  • Wannan mataki na tsaurara matakan tsaro dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shirye zaben gwamnan Osun a gobe Asabar, 15 ga Agusta, 2026
  • Za a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 3,763 da ke cikin mazabu 332 a kananan hukumomi 30 na jihar Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Yayin da jihar Osun ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a gobe Asabar, rahotanni sun nuna cewa an tsaurara matakan tsaro a ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da ke kan hanyar Gbongan-Ibadan a Osogbo.

Bayanai sun tabbatar da cewa an ga jami’an tsaro da dama a harabar ofishin INEC, ciki har da jami’an Rundunar ’Yan Sandan Najeriya.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Yan ssnda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a ofishin INEC na jihar Osun Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

Rahoton tashar Channels tv ya nuna ces ana kokarin kammala shirye-shiryen tura jami’an tsaron zuwa dukkan ƙananan hukumomi 30 na jihar domin tabbatar da tsaro yayin zaɓen.

Masu ruwa da tsaki sun isa INEC

Haka kuma, wasu masu ruwa da tsaki kan zaɓen sun isa ofishin hukumar domin halartar shirye-shiryen ƙarshe. aga cikinsu akwai ƙungiyoyin fararen hula, ’yan jarida da masu sa ido kan zaɓe.

An ce Kwamishinan Zaɓe na Jihar Osun, Oluwatoyin Babalola, na ganawa da kwamishinonin da kuma mataimakan kwamishinonin zaɓe daga wasu jihohi yayin da ake kammala shirye-shiryen zaɓen.

Za a yi zaɓe a rumfuna 3,763

Za a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 3,763 da ke cikin mazabu 332 a ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun.

INEC ta bayyana ranar Alhamis da ta gabata cewa sama da katunan zaɓe na dindindin (PVCs) miliyan 1.9 aka karɓa domin zaɓen gwamnan jihar.

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya ce adadin ya fito ne daga cikin jimillar masu rajista 2,339,233.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Umarnin da Tinubu ya ba INEC da 'yan sanda kan zaben Osun

Ya ce:

“Daga cikin jimillar masu rajista 2,339,233 a Osun, an karɓi katin PVC 1,906,390, wanda ya kai kashi 81.50 cikin 100. Sauran PVC 426,842, wato kashi 18.50 cikin 100, an ajiye su lafiya a Babban Bankin Najeriya (CBN)."
Disu.
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Hukumar ta kuma bayyana cewa wasu mutane da katunan PVC ɗinsu suka lalace, suka ɓaci ko suka ɓace sun nemi a sauya musu su.

INEC ta ce jimillar mutane 6,101 daga cikin wadanda suka nemi sauya katunansu sun buga kwafin PVC ɗinsu da za su iya saukewa.

Tinubu ya ja hankali kan zaben Osun

A wwni labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci INEC ta yi amfani da zaben gwamnan Osun wajen nuna shirinta na babban zaben 2027.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro da ke da hannu a zaben da su tabbatar da an gudanar da shi cikin lumana, gaskiya da tsari.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262