Shugaba Tinubu Zai Bar Abuja, Zai Shiga Kasashe 3 kafin Ya Dawo Gida Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya ta tsawon makonni biyu zuwa kasashen Faransa, Kenya da Rwanda
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa BolaTinubu zai halarci tarurruka kuma zai gana da shugabanni da yan kasuwa
- Tinubu zai tafi tare da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala taron a Rwanda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Asabar domin fara ziyarar kasashe uku da suka hada da Faransa, Kenya da Rwanda.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa wannan tafiya da Shugaba Tinubu zai yi zuwa wadannan kasashe za ta dauki tsawon makonni biyu.

Source: Facebook
Tinubu zai fara zuwa kasar Faransa
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a.

Kara karanta wannan
Dalilin da ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar rikicin sarautar Kano zuwa bayan zaben 2027
A cewarsa, shugaban kasar zai fara zuwa Faransa kafin daga bisani ya wuce birnin Nairobi na kasar Kenya domin halartar taron Africa-France Summit da zai fara mako mai zuwa.
Taron Africa-France Summit
Taron wanda shugabannin kasashen Faransa, Emmanuel Macron, da Kenya, William Ruto, za su jagoranta, zai mayar da hankali kan harkokin makamashi, bunkasa masana’antun da ke kare muhalli, fasaha da sauyin yanayi.
"Halartar taron da Tinubu zai yi daga ranar 11 zuwa 12 ga Mayu, 2026 zai nuna kudurin Najeriya na karfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka da Faransa," in ji sanarwar.
Taron zai hada shugabannin Afirka da na Faransa domin tattauna muhimman batutuwa kamar bunkasar tattalin arziki, kare muhalli, gina ababen more rayuwa, gina matasa da samar da zaman lafiya.
Abin da Tinubu zai yi a kasar Rwanda
Bayan kammala taron a Kenya, Tinubu zai wuce brinin Kigali na kasar Rwanda domin halartar taron Africa CEO Forum da za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu, 2026.
Taron na bana mai taken “Scale or Fail” zai hada manyan shugabannin kamfanoni, masu zuba jari da masana domin tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwa da zuba jari tsakanin kasashe.
An shirya taron ne tare da hadin gwiwar Hukumar International Finance Corporation (IFC), inda ake sa ran halartar sama da shugabanni da jami’ai 2,000.

Source: Twitter
A dukkan tarurrukan biyu, ana sa ran shugaba Tinubu zai gabatar da jawaban da za su bayyana sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin jawo hankalin masu zuba jari da bunkasa tattalin arziki.
Haka kuma zai gana da manyan shugabannin kasuwanci na duniya da na Afirka.
Tinubu zai tafi tare da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala taron a Rwanda.
Tinubu ya kare matakin ciyo bashi
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karbar bashi idan bukatar hakan ta taso.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Aso Rock yayin ganawa da masu ruwa da tsaki na jihar Plateau karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang.
Shugaban kasar ya ce karbo aron kudi ba aibu ba ne kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da karbowa idan akwai bukatar hakan.
Asali: Legit.ng
