Dino Melaye Ya Fadi 'Yan Siyasa 3 da Suka sayar da PDP ga Tinubu kafin Wike Ya Karasa Ta
- Tsohon Sanata Dino Melaye ya zargi wasu tsofaffin jami’an PDP uku da sayar da jam’iyyar ga Shugaba Bola Tinubu na APC mai mulki
- Sanara Dino Melaye ya ce tsofaffin shugabannin ne suka fara raunana jam'iyyar PDP mai adawa kafin Ministan Abuja, Nyesom Wike ya karasa rugujewar ta
- Tsohon sanatan ya yi wadannan zarge-zargen ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Kaa Truths podcast
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Sanata Dino Melaye, wanda ya wakilci Kogi ta Kudu a Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta takwas, ya zargi tsofaffin jami’an PDP uku da sayar da jam’iyyar ga Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa sun sayar da jam'iyyar ne kafin Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya shiga ya karasa abin da ya rage mata.

Source: Twitter
Dino Melaye ya yi wannan zargin ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Kaa Truths podcast, wadda ya sanya a shafinsa na X.
Wadanne mutane ne suka sayar da PDP?
Ya bayyana mutanen ukun da suka hada da Umar Damagum, tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa; Samuel Anyawu, tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa; da Umar Bature, wanda ya taba zama sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na kasa.
A cewar Melaye, mutanen ukun sun yi aiki wajen sayar da PDP ga Tinubu, sannan Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) kuma daya daga cikin manyan jiga-jigan rikicin cikin gida na jam’iyyar a baya-bayan nan, ya zo ya karasa rugujewar jam’iyyar.
Rikicin cikin gida na PDP
PDP ta kwashe shekaru tana fuskantar rikicin cikin gida, inda wasu magoya bayan jam’iyyar ke zargin wani bangare na shugabanninta da yin aiki da abin da ya saba wa muradun jam’iyyar daga cikin ta.
Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers, ya kasance daya daga cikin manyan jiga-jigan wannan rikici, musamman bayan ya yi fito-na-fito a fili da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, bayan zaben 2023.
Rikice-rikicen PDP sun jawo rarrabuwar kawuna a cikinta wanda hakan ya tilastawa manya jiga-jigai da dama daga cikinta suka fice.
Dino Melaye bai kawo hujja ba
Sababbin kalaman Melaye sun kara jawo wata muhawara kan wanda ya kamata a dora wa alhakin matsalolin da PDP ke fuskanta a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa.
Sai dai tsohon sanatan bai gabatar da wata takardar shaida da za ta tabbatar da zarge-zargen nasa ba yayin hirar.

Source: Facebook
Dino Melaye ya yi magana kan ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye, ya bayyana cewa jam'iyyar ADC za ta zaƙulo ɗan takarar da zai iya lallasa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Sanata Melaye ya ce duk da ADC ta tara manya-manyan jiga-jigan adawa, jam'iyyar ta shirya tsayar da wanda zai yi abin a zo a gani a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

