Yadda Matasan Najeriya Za Su Samu Tallafin N5m daga Gwamnatin Tinubu

Yadda Matasan Najeriya Za Su Samu Tallafin N5m daga Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin NiYA × Cascador, wanda zai bai wa wasu matasa ’yan kasuwa tallafin miliyoyi
  • Shirin zai horar da matasa ’yan kasuwa na tsawon makonni huɗu kan gudanar da kasuwanci, shirye-shiryen zuba jari, gabatar da ra’ayoyi da jagoranci
  • Masu neman shiga za su fara aikace-aikace ranar 19 ga Agusta 2026 ta shafin Nigerian Youth Academy, yayin da mafi ƙwazo za su samu tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon shiri da zai samar da tallafin kuɗi har Naira miliyan biyar ga zaɓaɓɓun matasa ’yan kasuwar Najeriya.

Shirin mai suna NiYA × Cascador Founders Programme, haɗin gwiwa ne tsakanin Nigerian Youth Academy ƙarƙashin Ma’aikatar Matasa da Ci Gaba da Cascador.

Gwamnatin Tinubu ta ware tallafi ga matasan Najeriya
Shugaba Bola Tinubi na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Ministan Matasa da Ci Gaba, Ayodele Olawande, ya sanar da shirin a shafinsa na Facebook ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Bayan zargin Trump, Musulmi da Kirista sun hadu a Abuja, an kulla yarjejeniya

Musabbabin tsara shirin saboda matasa

Olawande ya ce an tsara shi domin taimaka wa matasa ’yan kasuwa su shirya kasuwancinsu domin samun masu zuba jari da tallafin kuɗi.

A ƙarƙashin shirin gwaji, zaɓaɓɓun matasa ’yan kasuwa da ke matakin farko za su gudanar da horo mai zurfi na tsawon makonni huɗu.

Horon zai ƙunshi muhimman abubuwan kasuwanci, shirya kasuwanci domin samun jari, yadda ake gabatar da ra’ayin kasuwanci da kuma samun jagoranci kai tsaye.

A ƙarshen shirin, waɗanda suka nuna mafi kyawun aiki za su samu tallafin har Naira miliyan biyar kowannensu daga Cascador.

Masu cin gajiyar shirin za su kuma samu tsarin Enterprise Resource Planning (ERP), wanda zai taimaka musu wajen tsara, gudanar da faɗaɗa kasuwancinsu.

An fara shirin tallafawa matasa a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi yayin taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Amfanin da matasa za su samu kan shirin

A cewar ministan, an tsara shirin ne domin rage tazarar da ke tsakanin samun horo da damar samun jari ga matasa ’yan kasuwa.

Kara karanta wannan

An sanya sunayen 'yan takarar gwamna na ADC su 28 a shafin INEC

Musamman, shirin zai taimaka wa waɗanda ba su da isasshen tarihin kuɗi ko hanyoyin sadarwar da ake buƙata wajen samun tallafin kasuwanci.

Ya ce:

“Ba ma son mu tsaya kan horo kawai. Muna son gina wata hanya mai ƙarfi daga koyo zuwa kasuwanci, daga ra’ayoyi zuwa shirye-shiryen zuba jari, sannan daga baiwa zuwa kasuwanci mai dorewa.”

Ministan ya ƙara da cewa haɗin gwiwar ya samo asali ne daga tattaunawar da ma’aikatar ta yi da Cascador, ciki har da wani taron da ya shirya ranar 29 ga Afrilu.

Ya ce shirin ya nuna yadda irin waɗannan tattaunawa za su iya sauya zuwa samar da damarmaki na zahiri ga matasan Najeriya.

Yadda ake neman shiga tsarin?

Aikace-aikacen shiga NiYA × Cascador Founders Programme za su fara ne ranar Laraba, 19 ga Agusta 2026.

Matasa ’yan kasuwar Najeriya masu sha’awar shiga za su iya neman gurbin ta shafin [Nigerian Youth Academy] (https://niya.gov.ng/).

Masu neman shiga su sanya ido kan shafin daga ranar da aka buɗe aikace-aikacen domin samun cikakkun sharuɗɗan cancanta, fom ɗin neman shiga da kuma umarnin yadda za su gabatar da aikace-aikacensu.

Kara karanta wannan

'Don Allah, a bari mu sarara': Kwankwaso ya 'gano' shirin Tinubu kan zaben 2027

Sai dai babu tabbacin samun Naira miliyan biyar din domin za a bai wa waɗanda suka fi ƙwarewa kuma aka zaɓa ne kawai tallafin.

Gwamnatin Tinubu za ta tallafawa talakawa miliyan 3

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin HoPE-CT ya isa ga fiye da iyalai miliyan tara domin rage radadin talauci.

Ministan Yada Labarai, Idris Mohammed ya sanar da cewa za a bai wa iyalai miliyan uku da 600,000 tallafin N50,000.

A hannu daya, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce za a bada lamuni marar ruwa har N400,000 ga mata da matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.