Iran Ta Karyata Amurka kan asarar da Trump ya yi a Yaƙin Isra'ila, Ta Fadi Adadin Dalolin
- Ƙasar Iran ta zargi Amurka da karya kan kudin da aka kashe yayin yakin Jamhuriyar Musulunci da Isra'ila
- Iran ta ƙaryata wasu rahotanni kan asarar da Donald Trump ya yi tana cewa gwamnatinsa ta boye hakikanin adadin kuɗin
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce yakin ya jefa iyalan Amurka cikin karin kashe kudade, yana cewa kowane gida na biyan dala 500
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya zargi Amurka da boye hakikanin kudin yakin da ake yi da Isra'ila.
Araghchi ya bayyana cewa ana yada labaran karya kan asarar Amurka yana cewa Pentagon na karya kan adadin dalolin da aka kashe.

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafin X, Araghchi ya ce yakin ya riga ya lakume dala biliyan 100 daga aljihun masu biyan harajin Amurka.

Kara karanta wannan
Khamenei ya fusata game da barazanar Amurka, ya fadi shirin Iran kan makamin nukiliya
Yadda yaki ya barke tsakanin Iran, Isra'ila
Amurka da Isra’ila sun fara kai hare-hare kan Iran tun ranar 28 ga Fabrairun 2026 lamarin da ya jawo mayar da martani daga Tehran a yankin Gulf.
Iran ta kuma rufe mashigar ruwa na Hormuz bayan harin, abin da ya haddasa tashin hankali da matsin tattalin arziki a duniya baki daya.
Yaushe aka tsagaita wuta tsakanin Amurka, Iran?
An sanar da tsagaita wuta ranar 8 ga Afrilun 2026 ta hanyar shiga tsakanin Pakistan, sannan aka gudanar da tattaunawa a Islamabad.
Sai dai bangarorin biyu sun kasa cimma yarjejeniya bayan tattaunawar, duk da kokarin Pakistan na ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakanin kasashen.
Daga baya shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ba tare da saka sabon wa’adi ba, bisa bukatar Pakistan.

Source: Getty Images
Zargin da Iran ke yi kan Netanyahu
Ya ce Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne ya jefa Amurka cikin wannan tsadar, yana cewa abin da ake kira “Israel First” na cutar da Amurka.

Kara karanta wannan
Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25
Araghchi ya kara da cewa asarar kai tsaye kadai ba ce matsalar ba, domin iyalan Amurka na ci gaba da fuskantar karin kudin rayuwa kullum.
A ranar Laraba 29 ga watan Afrilun 2026, jami’in Pentagon Jules Hurst ya bayyana wa majalisa cewa aikin “Operation Epic Fury” ya kashe kusan dala biliyan 25 kacal zuwa yanzu.
Sanarwar ta ce:
“Ma’aikatar tsaron Amurka tana karya. Cacar da Netanyahu ya yi ta jawo wa Amurka asarar dala biliyan 100 zuwa yanzu, wanda ya ninka sau hudu fiye da abin da ake ikirari.
"Asarar da masu biyan haraji a Amurka za su dauka a fakaice ta fi haka yawa sosai kudin da ke hau kan kowanne gidan Amurkawa a wata ya kai dala 500 kuma yana ci gaba da karuwa cikin sauri."
Iran ta godewa Pakistan kan sulhu da Amurka
A baya, an ji cewa gwamnatin Iran ta mika sakon godiya ga Pakistan bisa yadda ta yi ruwa ta yi tsaki a kokarin sulhunta kasar da Amurka.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan bayan ya karbi tawagar Pakistan da ta kai ziyara Tehran.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an Iran sun shiga ganawa da tawagar Pakistan kuma ana sa ran za a yi maganar komawa tattaunawa da Amurka.
Asali: Legit.ng