Isra'ila Ta Yi Iƙirarin Kashe Kwamandan Hamas bayan Ya Shirya Hallaka Sojojinta
- TtttRahotanni daga Isra'ila sun tabbatar da cewa wai sun yi nasarar hallaka wani kwamandan Hamas a Gaza
- Rundunar Isra’ila ta ce kwamandan ya samu munanan raunuka a harin sama da ta kai wani maboyar Hamas a Gaza ranar 30 ga Yuli
- A cewar rundunar, Mushtaha na daga cikin mutanen da suka rike garkuwa da dama, sannan yana shirin kai hare-hare kan sojojin Isra’ila da fararen hula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Rundunar tsaron Isra’ila (IDF) ta ce ta yi nasarar hallaka wani kwamandan Hamas a yankin Gaza.
An ce Muhammad Bassam Muhammad Mushtaha, kwamandan Hamas, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wani harin sama.

Source: Facebook
Al Jazeera ta ce Mushtaha ya shiga harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, sannan ya rike wasu mutane a matsayin garkuwa a Gaza.

Kara karanta wannan
Malamin jami'a ya shiga matsala bayan ya ce masu Keke napep sun fi farfesa samun kudi
Mushtaha ya kasance kwamandan wani runduna a Bataliyar Shati, wadda ke karkashin bangaren soji na Hamas.
Rundunar Isra’ila ta ce Mushtaha ya samu munanan raunuka a wani harin sama da aka kai kan wata maboya a Gaza ranar 30 ga Yuli.
Bayan kwanaki da dama, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu daga harin, a cewar sanarwar da rundunar Isra’ila ta fitar.
Rundunar ta ce a lokacin yakin, Mushtaha yana da hannu wajen tsare wasu garkuwa da dama a Gaza.
Daga cikin mutanen da aka ce yana da hannu wajen tsare su akwai Tsachi Idan, Kofur Noa Marciano, Ziv Berman, Omri Miran, Ori Megidish, Naama Levy da Matan Angrerst.
Rundunar Isra’ila ta ce Mushtaha ya kuma shiga yunkurin shirya sabbin hare-haren ta’addanci kan sojojin Isra’ila da fararen hula.
Ta ce an kai harin ne domin kawar da barazanar da yake wakilta ga sojoji da fararen hula, cewar Times of Israel.
Rundunar ta ce:
“Dan ta’addan ya yi kokarin ciyar da gaba da hare-haren ta’addanci kan sojojin IDF da fararen hular Isra’ila, sannan aka kawar da shi domin cire barazanar. “Sojojin IDF da ke karkashin rundunar Kudanci suna ci gaba da kasancewa a yankin bisa yarjejeniyar, kuma za su ci gaba da aiki domin kawar da duk wata barazana.”

Kara karanta wannan
Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2
A halin da ake ciki, Jared Kushner, wakilin musamman na Amurka, da Nikolay Mladenov, babban darektan Hukumar Zaman Lafiya ta Gaza, na shirin ziyartar Isra’ila.
Rahotanni sun ce mutanen biyu za su tattauna da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan yadda za a fara aiwatar da shirin Trump mai maki 15 kan Gaza.
Ana sa ran za su iya zuwa Isra’ila mako mai zuwa, sai dai wata majiya da ta san batun ta ce har yanzu ba a kammala tabbatar da ziyarar ba.
Amurka ta sake caccakar Isra'ila
An ji cewa Gwamnatin Donald Trump ta soki Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, bayan ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa a kudancin Lebanon.
Amurka ta ce zaman sojojin Isra’ila na dindindin a kudancin Lebanon ya saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma da kuma alkawarin mutunta Lebanon.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta jaddada goyon bayanta ga cikakken ikon mallakar Lebanon da kuma kare mutuncin iyakokinta.
Asali: Legit.ng