Saboda Wa'azin Sheikh Jingir, Wata Za Ta Zabi APC duk da ba ta Son Tinubu

Saboda Wa'azin Sheikh Jingir, Wata Za Ta Zabi APC duk da ba ta Son Tinubu

  • Wata ta ji shawarar Sani Yahaya Jingir, ta ce babu abin da zai hana ta zaben Bola Tinubu da Kashim Shettima a badi
  • Amina Aliyu Kwararre ba ta cikin masu kaunar shugaban Najeriyan amma tana yi wa Izalar Jos biyayya ta kin karawa
  • Har buri Amina Kwararre ta yi a ce namiji ce ita saboda yadda ta ga maza sun kyale ana sukar babban malamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Jos - Wata Baiwar Allah ta fito ta sanar da duniya zabinta idan an fito takara a zaben shekara mai zuwa a Najeriya.

Amina Aliyu Kwararre tana cikin wadanda jira kawai suke yi a fita filin zabe su ba Bola Ahmed Tinubu kuri’arsu.

Tinubu
Bola Tinubu yana jawabi da Sani Jingir wajen wani taro Hoto: Olusegun Dada/Ibrahim Maina Muhammad
Source: Facebook

Amina Kwararre za ta zabi Bola Tinubu

A shafinta na Facebook muka ci karo da Amina Aliyu Kwararre tana cewa da yardar Allah SWT sai ta zabi APC a 2027.

Kara karanta wannan

ADC: 'Abu 1 da zai hana jam'iyyar su Atiku nasara a zaɓen Osun'

Dalilinta ba komai ba ne kuwa illa kiran da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi na a goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi.

Matar ta lura da yadda aka taso jagoran na kungiyar Izala a gaba, ta yi tir da mazan da suka yi shiru ana yi masa raddi.

Abin da ya fi jan hankali shi ne, Amina Aliyu Kwararre ta ce ita ba ta taba kaunar Tinubu, amma za ta zabe shi a badi.

Kuma ta ce duk wata macen da za ta zo shafin nata a Facebook ta soke ta saboda wannan matsayar, daidai ta ke da ita.

Shawarar Sheikh Sani Jingir ta yi aiki

Matar ta rubuta:

"Tinubu be ta6a birge ni ba, ban ta6a son shi ba, amma 2027 insha Allah babu abin da zai hana ni za6an tinubu domin bin shawarar malam.
"Wanda ya ji haushi ya hadiyi zuciya."

Kara karanta wannan

Shi ne mafi munin shugaban kasa a tarihi in ji tsohon hadimin Tinubu

A bayaninta, ta hada da mazan kungiyar Izala mai hedikwata a Jos, ta ce:
"Ku mazajen nan na JIBWIS NHQ Jos ba ku ta6a bata mani rai ba kaman wannan lokacin, tsoron waye kuke ji da ba za ku iya yi wa kowa raddi ba?
"Amma kun noke kuna gani ana zagin dattijo sai dai kuyi wani kwaments da bai wuce layi biyu ba, rubutun aka fi ku iyawa ko meye??
"Ban ta6a burin ina ma a ce ni namiji ne ba mace ba kaman a wannan lokacin Wallahi."

Wata yar Izala ta bijire wa Jingir

Duk da haka, mutane irinsu Fatima Abubakar Sidi sun maida mata martani nan-take, suka ce babu su babu Tinubu a zaben 2027.

Fatima Sidi ta ce ita ma yar Izala ce, amma ba za a yaudare ta da tikitin Musulmi da Musulmi ba saboda matsalar rashin tsaro.

“Ai wlh ba mahalukin da ya Isa ya sa ni zaban Tinubu duk duniyan nan
“Ni yar Ahlussunnah ce Kuma yar izala, zan girmama mallam duk zagin da ake yi masa Wallahi a raina na ke ji tunda yancin shi ne, amman fa ba zan bi abi nda yace na zaben Tinubu ba

Kara karanta wannan

ADC ta ji kamshin hadakar 'yan adawa, ana son tsayar da dan takara 1 ya tunkari Tinubu

"Ni yar Maiduguri ce haifaffiyar Maiduguri can na ta so naga Boko Haram na ga bala'in ta amman fa banga tashin hankalin da ya kai na bandits ba.

Fatima Sidi ta bada labarin ta'adin 'yan bindiga:

"Aure ya kawo ni Katsina ina da ciki wata takwas, bandits suka shiga anguwarmu ina jin su jikin tagar dakina; daya yana cewa ka harba daya yana cewa kar ka harba.
"Ga mace mai ciki dajin fitsari ga shi tashin hankali ya karu duk biyan minti 15 sai na ji fitsari haka na rika sake fitsari kan gado saboda in suka ji motsi kadan to Wallahi sai dai wani ikon Allah. Ga wani azabar ciwon cikin daya tashi mani.
"Wallahi tun 11:00 na dare suka shigo suna ta harbi da kashe mutane su ne ba su tafi ba sai 3:00 na dare. A lokacin sun kwashe neighbors dina Wallahi Tallahi dayar da cikinta suka tafi da ita a wurinsu ta haihu, wai su ka sama dan sunan ogansu."

Ita wannan mata ta zauna a Maiduguri, amma ba ta taba ganin tashin hankali irin na ‘yan bindiga ba don haka ba ta tare da Sheikh Jingir.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Sheikh Jingir ya yi ƙarin bayani kan kalamansa da suka tayar da ƙura a Najeriya

Muslim-Muslim:Shugaban Izala ya sha rubdugu

An ji labari cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya sha suka daga jama’a ta ko ina a sanadiyyar tallata Bola Tinubu da Kashim Shettima da yake yi.

Rabiu Musa Kwankwaso ya soki kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2027 da ya ziyarci Kano.

Don haka, ya yi kira ga shugabannin addini da na siyasa da su mayar da hankali wajen inganta zaman lafiya da haɗin kan ƴan kasa ba kawo sabani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng