Bello Matawalle Ya Je Wajen Kera Makamai a Masar, ana Neman Haɗaka da Najeriya

Bello Matawalle Ya Je Wajen Kera Makamai a Masar, ana Neman Haɗaka da Najeriya

  • Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa muhimman masana’antun tsaro a Masar domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu
  • Tawagar ta duba hanyoyin haɗin gwiwa wajen kera kayan aikin soji a Najeriya da kuma ƙara ƙwarewar fasaha da sauya ilimin masana’antu zuwa cikin ƙasar
  • Ziyarar ta kuma mayar da hankali kan yiwuwar kafa wajen kera harsasai a Najeriya ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Karamin Ministan Tsaro, Dr Bello Muhammed Matawalle, ya jagoranci wata babbar tawagar Najeriya zuwa ziyarar kwanaki biyu a wasu muhimman masana’antun tsaro a Masar.

Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da Masar da kuma bunƙasa masana’antun kera kayan aikin tsaro a cikin gida.

Kara karanta wannan

Bayan zargin Trump, Musulmi da Kirista sun hadu a Abuja, an kulla yarjejeniya

Bello Matawalle a Masar
Tawagar Najeriya a kasar Masar. Hoto: Federal Ministry of Information and National Orientation, Nigeria
Source: Facebook

Ma’aikatar yada labarai ta wallafa a Facebook cewa ziyarar ta kuma yi daidai da shirin Najeriya na ƙara dogaro da kanta wajen samar da kayan aikin soji da rage dogaro da ƙasashen waje.

Me Bello Matawalle ya je yi Masar?

Rahoto ya nuna cewa a ranar farko ta ziyarar, tawagar Najeriya ta kai ziyara masana’antar makamai ta Eagle da ke Suez.

Tawagar ta duba wasu daga cikin na’urori da kayan aikin tsaro da kamfanin na Masar ke samarwa, tare da samun damar fahimtar tsarin samar da kayan aikin soji.

Matawalle ya ce ziyarar ba ta mayar da hankali kan sayen kayan aikin soji nan take ba, sai dai binciken hanyoyin samar da haɗin gwiwar masana’antu mai ɗorewa.

Najeriya na son haɗin gwiwa

Ministan ya ce babban burin Najeriya shi ne ƙulla haɗin gwiwa da Masar, musamman ta hannun Hukumar Masana’antun Tsaro ta Najeriya, DICON.

Kara karanta wannan

Sababbin rundunonin soji 4 za su fara aikin kakkabe 'yan ta'adda

PR Nigeria ta wallafa cewa ya ce haɗin gwiwar zai iya bai wa ƙasashen biyu damar haɗa kai wajen kera wasu kayan aikin soji da na’urorin tsaro a Najeriya.

Matawalle ya ce hakan zai taimaka wajen ƙara ƙarfin masana’antun Najeriya da bunƙasa ƙwararrun ma’aikata a fannin fasahar tsaro.

Batun kera harsasai a Najeriya

A rana ta biyu, tawagar Najeriya ta gana da Ma’aikatar Samar da Kayan Soji ta Masar a birnin Alkahira.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan fannoni daban-daban na haɗin gwiwa, musamman yiwuwar kafa wajen kera harsasai a Najeriya.

Bangarorin biyu sun nuna sha’awar ci gaba da wannan haɗin gwiwa tare da yin aiki domin kulla yarjejeniyoyin da za su samar da tsarin aiwatar da shirin.

Ma’aikatar Tsaro ta ce shirin ya yi daidai da manufar Najeriya ta samun cikakken dogaro da kanta wajen samar da muhimman kayan aikin tsaro.

Bello Matawalle a ofis
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr Bello Matawalle
Source: UGC

Ta ce hakan zai rage dogaro da wasu ƙasashe wajen samar da makamai da kayan aikin soji, tare da ƙara ƙarfin rundunonin tsaron Najeriya.

An kama masu garkuwa a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna ta kama mutane shida da ake zargi da garkuwa da mutane tare da tarwatsa wata maboyar masu garkuwa a ƙaramar hukumar Ikara.

Kara karanta wannan

Hukumar alhazai ta sanar da kuɗin kujerar hajjin shekarar 2027 a jihar Kano

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an kama mutanen ne bayan wani da aka yi garkuwa da shi ya tsere daga hannunsu tare da bai wa ‘yan sanda bayanai.

Ya ce wanda aka sace ya shaida wa ‘yan sanda cewa an tsare shi a wani gida mallakar wani mai suna Ja’e Samalu, mai shekaru 65, a ƙauyen Dogon Pako da ke Ikara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng