Gwamna Diri Ya Tsige Mai Martaba Sarki a Najeriya, Ya Rushe Majalisar Sarakuna

Gwamna Diri Ya Tsige Mai Martaba Sarki a Najeriya, Ya Rushe Majalisar Sarakuna

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayar da umarnin tsige sarkin Ogboinbiri, Okosughe Benson Eseimokumo, tare da rushe majalisar sarakuna
  • Wannan mataki ya biyo bayan rikicin ranar Talata da ya yi sanadin asarar rai da kone-kone a garin na Ogboinbiri da ke ƙaramar hukumar Southern Ijaw
  • Tun kafin a sanar da tsige sarkin, gwamnati ta sanya dokar ta-ɓaci ta awanni 12 domin dawo da zaman lafiya a garin da ake hako man fetur

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bayelsa – Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya ɗauki tsauraran matakai a ranar Alhamis kan masarautar Ogboinbiri sakamakon rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a yankin.

Gwamnan ya sanar da tsige mai martaba Sarkin Ogboinbiri, Chief Okosughe Benson Eseimokumo, da kuma rushe majalisar sarakuna, kwamitin CDC, da kuma ƙungiyar matasa ta garin baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Duk da Allah wadan Abba, matar da ta jagoranci ɗaga kamfai ta samu mukami a Kano

Gwamna Douye Diri ya tsige sarki saboda rikici
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa. Hoto: @govdouyediri
Source: Facebook

Gwamna ya tsige sarki a Bayelsa

Tsige mai martaba sarkin da rushe majalisar sarakunan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Dan Alabrah ya fitar, in ji rahoton NTA.

A cewar Dan Alabrah, dama can gwamnatin jiha ba ta riga ta ba wa Chief Eseimokumo cikakken ikon sarauta ba saboda rigingimun da suka daɗe suna addabar yankin.

Sanarwar ta ce Gwamna Douye Diri ya sanar da tsige sarkin ne a lokacin taron yabon ubangiji na watan Afrilu da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Yenagoa.

Domin tabbatar da cewa al'amuran garin ba su tsaya ba, gwamnan ya umarci mataimakinsa, Dr. Peter Akpe, da kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu da su kafa kwamitin riƙon ƙwarya da zai kula da masarautar Ogboinbiri har sai zaman lafiya ya dawo.

An ayyana dokar ta baci a Bayelsa

Kazalika, ya umurci kwamishinan ƴan sanda na jihar da ya tabbatar an kamo duk waɗanda ke da hannu a rikicin ranar Talata domin su fuskanci shari'a.

Kara karanta wannan

Abba ya kinkimo aiki, za a kashe sama da N21bn don jiƙa Kanawa da ruwan sha

Tuni dai gwamnatin jihar ta sanar da sanya dokar ta-ɓaci a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2026, wadda ke fara aiki daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe kowace rana.

Kwamishinar yaɗa labarai, Hon. Ebiuwou Obiyai, ta bayyana cewa wannan dokar za ta ci gaba da aiki har sai yadda hali ya yi, in ji rahoton Punch.

Ana ci gaba da samun rikice-rikice a garuruwan da ake hako man fetur a Bayelsa.
Taswirar jihar Bayelsa, inda gwamna ya tsige sarki saboda tashe tashen hankula. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rikicin man fetur a yankunan karkara

Gwamna Diri ya nuna matsananciyar damuwa kan yadda rikice-rikice ke ɓallewa a yankunan da ake hako man fetur sakamakon raba kuɗaɗen da kamfanonin mai ke bayarwa.

Ya bayyana waɗannan kuɗaɗe a matsayin "'yan canji" idan aka kwatanta su da irin ribar da kamfanonin ke samu a yankunan, inda ya yi kira ga al'umma da su daina zubar da jini a tsakaninsu saboda waɗannan kuɗaɗe.

Rikicin ranar Talata ya tilasta wa mazauna garin da dama tserewa daga gidajensu zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu, lamarin da ya jefa yankin cikin fargaba da rashin tabbas.

Diri ya dakatar da sarkin Swali

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Douye Diri ya dakatar da Sarkin Swali, Mai Martaba Wilcox Seiyefa Job sakamakon taɓarɓarewar tsaro.

Kara karanta wannan

OPEC+: UAE ta dauki mataki 1 da ya girgiza Saudiyya da kasuwar mai ta duniya

A wata sanarwa da gwamnatin Bayelsa ta fitar, ta ce an dakatar da basaraken saboda yadda ya gaza shawo kan ayyukan kungiyoyin asiri.

Gwamnatin jihar Bayelsa ta buƙaci ƴan sanda su gaggauta kama duk mai hannu a lamarin ciki har da ƴaƴan sarkin guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com