2027: Alamu Sun Nuna Kwankwaso da Obi za Su Fita daga Jam'iyyar ADC

2027: Alamu Sun Nuna Kwankwaso da Obi za Su Fita daga Jam'iyyar ADC

  • Alamu sun nuna cewa 'yan Kwankwasiyya da ke shirin hada kai da Peter Obi na iya sauya sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta ADC
  • Manyan 'yan Kwankwasiyya, Dr Yusuf Kofarmata da Sanata Rufa'i Hanga sun nuna cewa har yanzu jam'iyyar ADC na cikin rikici
  • Masana da dama sun fara gargadin Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi kan shirin sauya sheka da ake hasashen za su yi kafin 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Manyan jagororin tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Kwankwaso ke jagoranta sun fara nuna damuwa kan halin da jam'iyyar ADC ke ciki.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa suna jiran matakin da Rabiu Kwankwaso zai dauka domin ganin ba su zama 'yan kallo ba a 2027.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An je kotu an nemi a soke rajistar ADC, wasu jam'iyyu 4

Peter Obi Rabiu Rabiu Musa Kwankwaso
Peter Obi Rabiu Rabiu Musa Kwankwaso a taron ADC a Kano. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

ADC: Kofarin 'yan Kwankwasiyya

Daya daga cikin na hannun daman Kwankwaso, Dr Yusuf Kofar mata ya wallafa a Facebook cewa jam’iyyar ADC tana fama da rikice-rikice da dama.

Ya ce:

"Zai zama abin mamaki idan jam’iyyar ta tsira daga matsalolin cikin gida da na waje a halin yanzu, wadanda ke barazana ga hadin kanta da cigabanta a matsayin jam’iyyar adawa."

A kan batun Batun Nafi’u Bala, Dr Yusuf ya ce:

"Duk da cewa Kotun Koli ta yanke hukunci, yana da hadari a dauki hakan a matsayin nasara; mayar da shari’ar zuwa Babbar Kotun Tarayya domin ci gaba da sauraron karar hukunci ne mai hatsari ga jam’iyyar.
"Abin da Kotun Koli ta soke shi ne umarnin ci gaba da matsayin da ake ciki kawai, amma babban batun da ke gaban kotu yana nan yana gudana.
"Ba a san abin da zai biyo baya ba karkashin tasirin wannan dan siyasa mai taurin kai kamar yadda yake kiran kansa.

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

Game da rikici a Kano kuwa, ya ce:

"Wani bangare na jam’iyyar a Jihar Kano ya kai jam’iyyar kara a Babbar Kotun Jiha: kotun da ta zauna ranar Litinin ta dage sauraron karar na tsawon wata guda."

Shi ma a na shi bangaren, Sanata Rufa'i Hanga da ke tare da Kwankwaso ya ce wanda bai san halin da ake ciki ba ne zai ga kamar ADC ce ta yi nasara a Kotun Koli.

A wata hira da tasahar Kwankwasiyya Talk Show ya yi da shi a Facebook, Sanata Hanga ya ce suna jira Kwankwaso ya nuna musu jam'iyyar da za su koma.

Yadda aka yi zanga-zangar ADC a Najeriya
Rabiu Kwankwaso da Peter Obi wajen zanga-zangar ADC a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Gargadin da ake yi wa Kwankwaso

Fitaccen dan jarida, Jafar Jafar ya yi gargadi ga Rabiu Kwankwaso da Peter Obi kan komawa NDC daga jam'iyyar adawa ta ADC a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Ya ce:

"Babban kuskuren siyasa da Obi da Kwankwaso za su yi shi ne rabuwa da hadakar ADC. Ko da mutum yana da kwarewar jagoranci, mutane ba sa binsa har kabari. Matukar ADC tana nan da rai, NDC ba za ta yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Ana jiran hukuncin kotu: David Mark ya fadi abin da zai faru da ADC a zaben 2027

"Idan APC za ta iya saka Nafiu cikin babbar hadakar jam’iyyun adawa ta ADC, me ya sa kuke ganin ba za su iya kirkirar wani Nafiu a NDC ko PRP domin tarwatsa su ba?

Ya ce shawarar da zai ba su ita ce:

"Ku zauna a ADC ku yi gwagwarmaya tare. Jirgi ba zai iya tafiya gaba ba idan kowa yana tuƙa shi ta hanyarsa daban.
"Kayar da jam’iyya mai mulki kamar APC da dan siyasa irin Tinubu ba abu ne mai sauki ba, ko da dukkan jam’iyyun siyasa a Najeriya sun hada kansu."
Manyan ADC a wajen taro
Jagororin ADC a wajen taron da suka yi a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Dan Kwankwasiyya da ya yi fice a kafafen sada zumunta, Musbahu Baffa ya nuna cewa akwai hadari a ce Kwankwaso da Obi sun sauya sheka.

Sakon da ya wallafa a Facebook ya ce:

"Matuƙar Obi da Kwankwaso za su ware kan su daga Atiku, babu shakka ba su da bambanci da Nafi'u da ya kawo tarnaƙi a jam'iyyar ADC.
"Duk wani mataki ko hukunci da za a zartar ba tare da Atiku ba, tabbas an zo da tsantsar son zuciya a wannan gaɓar da muka tsinci kan mu!

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

"A jira saƙo na gaba!"

Atiku ya gargadi Tinubu kan 2027

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan zaben 2027.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa yunwa, rashin tsaro da sauran matsalolin da Bola Tinubu ya gagara magancewa za su jawo ya fadi zabe.

Martanin Atiku ya zo bayan shugaban kasar ya nuna cewa ana masa makarkashiya game da tazarce da ya ke nema amma kuma zai yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng