Wasu 'Yan Arewa Sun Fara Adawa Mai Karfi da Muslim Muslim a 2027
- Kungiyoyin fararen hula sama da 80 sun yi watsi da shirin kafa wuraren kiwon shanu na musamman da gwamnatin tarayya ke son yi
- Sun kuma yi fatali da tikitin shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi, suna masu cewa hakan ya saɓa wa tsarin addinai daban-daban na Najeriya
- Kungiyoyin sun ayyana dokar ta-ɓaci kan kashe-kashen da ake cewa sun addabi Wasu ‘Yan Arewa ta Tsakiya, tare da neman gwamnati ta kare al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Ƙungiyar Middle Belt Concern, wadda ta haɗa kungiyoyin fararen hula sama da 80, ta yi watsi da shirin kafa wuraren kiwon shanu na musamman da kuma tikitin shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi.
Ƙungiyar ta ce waɗannan matakai ba su dace da muradun al’ummomin da lamarin ya shafa ba, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa kan matsalar tsaro.

Source: Twitter
Warewa masu shanu wurin kiwo
Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta ƙi amincewa da shirin kafa wuraren kiwon shanu na musamman, tana mai cewa al’ummomin da rikicin ya shafa na buƙatar komawa gidajensu na asali.
Ta ce kafa irin waɗannan wurare ba zai magance tushen matsalar ba, kuma zai iya ƙara raba al’umma da filayensu.
Kakakin kungiyar, Jonathan-Ichaver ta ce:
“Dole gwamnati ta tabbatar da tsaron al’umma, ta samar da kulawa ga waɗanda abin ya shafa, sannan ta tsara hanyar da za a bi wajen dawo da mutanen da aka raba da muhallansu.”
Batun Muslim Muslim a 2027
A kan tikitin shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi, Jonathan-Ichaver ta ce ƙungiyar ta yi watsi da tsarin saboda tana ganin ya saɓa wa tsarin Najeriya na kasancewa da addinai daban-daban.
Ta ce:
“Mun yi watsi da tikitin Musulmi da Musulmi da gwamnatin yanzu ta tilasta wa wannan ƙasa.”
Ta bayyana tsarin a matsayin abin da ya yi watsi da tsarin addinai daban-daban da kuma daidaiton da ya taimaka wajen haɗa ƙasar.
Jonathan-Ichaver ta kuma yi watsi da bayyana hare-haren da ake kai wa al’ummomin yankin da sunan rikicin manoma da makiyaya ko rikicin al’umma.

Source: Original
Ta ce irin wannan bayani bai bayyana girman da tasirin hare-haren da al’ummomin yankin ke fuskanta ba.
Ta ce abin da ke faruwa ba rikici ba ne tsakanin maƙwabta, tana mai zargin cewa hare-haren wani nau'in tashin hankali ne da ake maimaitawa kuma ke ƙaruwa.
Al-Issa ya gana da Bola Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi Shugaban Ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Sheikh Dr Mohammed Al-Issa, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A yayin ganawar, shugabannin sun tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan ƙungiyar, musamman shirin samar da zaman lafiya a Afirka ta Yamma.
Tinubu ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar Abuja da shirye-shiryen aiwatar da ita, yayin da taron ya haɗa malaman Musulmi da Kiristoci daga ƙasashen Afirka ta Yamma.
Asali: Legit.ng

