Maganin Mallaka: Matashin da Ya Birne Kur'ani da Wasu Kayan Tsubbu Ya Shigo Hannu
- ’Yan sanda a Kebbi sun kama wani Abubakar Musa mai shekara 29 bisa zargin aikata laifin haɗa baki, cin zarafin littattafan addini da kuma da tsafe-tsafe
- Ana zargin wanda ake zargin da wasu mutum biyu da binne kwafin Alƙur’ani tare da maniyyi, goro da wasu abubuwan tsafi a cikin ɗakin wata mata a Zuru
- ’Yan sanda na neman sauran waɗanda ake zargi, yayin da Abubakar Musa ke tsare kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta kama wani Abubakar Musa, mai shekara 29, ɗan ƙauyen Rafin Mose da ke ƙaramar hukumar Zuru, bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, cin zarafin littattafan addini, amfani da tsafi da kuma haddasa rikici.
Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 14 ga watan Agusta, 2026 inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 9 ga Agustan 2026 da 7 na dare a yankin Zango da ke Zuru.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa a cewar sanarwar, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da wasu mutane biyu, Rabi’u Tela, mijin Zarau Hassan, da Hamza Zango, waɗanda suka tsere, wajen haƙa rami a cikin ɗakin Zarau Hassan.
An kama matashi a Kebbi
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa ana zargin sun birne kwafin Alƙur’ani a cikin ramin tare da maniyyi, farin goro da jan goro, kayan sawa na ƙasa, matattun dabbobi da wasu abubuwan tsafi.
Sai dai ’yan sanda sun ce yadda aka gudanar da wannan aiki na da yuwuwar tayar da hankali da kawo ɓarkewar tashin hankali tsakanin al’ummar Musulmi a yankin.
Rundunar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke Rabi’u Tela da Hamza Zango, yayin da Abubakar Musa ke tsare a hannun ’yan sanda.
Yan sandan Kebbi sun yi magana
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, CP Umar M. Hadejia, ya yi Allah-wadai da abin da ake zargin mutanen sun aikata, yana mai cewa rundunar za ta ɗauki matakin da ya dace bisa doka.

Source: Original
Umar M. Hadejia ya kara da cewa za a saka kafar wando daya da duk wanda ke aikata abin da zai jawo rikici na addini da tayar da hankulan jama'a.
Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suke zargi ga ’yan sanda cikin gaggawa, tana mai tabbatar da cewa za a kiyaye sirrin masu bayar da bayanan.
An samar da masarautu a Kebbi
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da kafa sabuwar gunduma mai kunshe da yankunan kauyuka takwas a karamar hukumar Dandi don fadada masautar.
Dr. Nasir Idris ya kuma amince da nada sabon mai unguwa a karamar hukumar Augie domin karfafa tsarin mulkin gargajiya da inganta shugabanci a matakin kasa da ke kusa da jama'a.
Gwamnan ya kuma nada mutumin da zai jagoranci sabuwar gundumar da aka kafa domin gudanar da harkokin mulki, sannan ya mika sako da sababbin sarakunan da aka nada a yankunansu.
Asali: Legit.ng

