Malamin Jami'a Ya Shiga Matsala bayan Ya Ce Masu Keke Napep Sun Fi Farfesa Samun Kudi

Malamin Jami'a Ya Shiga Matsala bayan Ya Ce Masu Keke Napep Sun Fi Farfesa Samun Kudi

  • Jami’ar Jihar Abia (ABSU) ta dakatar da wani malaminta, Farfesa Nnamdi Nwaeze daga aikin koyarwa har sai an gama bincike
  • An dakatar da shi ne kan wani rubutu da ya yi a kafar sada zumunta, inda ya ce masu Keke Napep sun fi farfesoshi samun kudi a wata
  • Shugabancin jami’ar ya kuma kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Jami’ar Jihar Abia (ABSU) ta dakatar da wani malami, Farfesa Nnamdi Nwaeze, daga Sashen Tattalin Arziki da ke karkashin Faculty of Economics and Management Sciences.

Mai magana da yawun jami’ar, Chijioke Nwogu, ne ya sanar da dakatarwar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta, 2026.

Jami'ar Abia.
Kofar shiga jami'ar jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya Hoto: Blessed Pen
Source: Facebook

An dakatar da Nwaeze, wanda farfesa ne, bayan wani rubutu da ya wallafa a Facebook, inda ya yi ikirarin cewa malaman jami’ar da ke matsayin farfesoshi suna samun kasa da N400,000 a wata.

Kara karanta wannan

Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2

Farfesan ya yi magana kan albashi

Rubutun malamin ya shafi yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta ayyana a ABSU.

Nwaeze ya ce yana da masaniya kan batutuwan da suka haddasa yajin aikin, amma ya zabi kada ya bayyana su saboda gudun kada a yi masa kallon “makiyin gwamnati” ko kuma a kore shi bisa zargin yin kalaman siyasa.

Ya kuma yi ikirarin cewa malaman ABSU na karbar albashi mafi karanci idan aka kwatanta da takwarorinsu a sauran jami’o’in Najeriya.

Masu Napep sun fi farfesa samun kudi

A cewarsa, har yanzu ana biyan malaman jami’ar bisa tsarin albashin ASUU da gwamnatin tarayya na shekarar 2009, maimakon sabon tsarin da aka tsara a shekarun baya.

Nwaeze ya yi ikirarin cewa farfesoshi a ABSU suna samun kasa da N400,000 a wata, yayin da masu tuka Keke Napep mai kafa uku ke iya samun sama da N450,000.

Ya kuma ce:

Kara karanta wannan

Duka bayanan da suka fito daga juyin mulkin da aka yi yunkurin yi wa Tinubu

“Shin kun san cewa farfesoshi a dukkan jami’o’in tarayya da mafi yawan jami’o’in jihohi yanzu suna samun tsakanin N1.3m zuwa N1.4m, sabanin abin da ake samu a ABSU?”

Ya kara da ikirarin cewa wasu ‘yan majalisar kananan hukumomi da na jihohi da kuma wasu masu rike da mukaman gwamnati suna samun albashi da alawus-alawus masu yawa idan aka kwatanta da malaman jami’ar.

Farfesa Nnamdi Nwaeze.
Malamim jami'ar jihar Abia da aka dakatar, Farfesa Nnamdi Nwaeze Hoto: Nnamdi Nwaeze
Source: Facebook

ABSU ta ce rubutun ya saba mata

A cikin sanarwar, Nwogu, wanda shi ne mataimakin rajistaran jami’ar, ya ce rubutun da malamin ya wallafa a kafar sada zumunta “ya sabawa muradun jami’ar kuma bai dace da masu kula da jami’ar ba.”

Shugabancin jami’ar ya kuma kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Nwogu ya ce:

“Dakatarwar ta fara aiki nan take, har sai an kammala binciken kwamitin.”

ASUU na shirin tafiya yajin aiki

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar ASUU ta ƙasa ta umarci jami’o’in jihohi kusan 20 su fara yajin aiki na sai baba-ta-gani cikin makonni biyu masu zuwa.

ASUU ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda gaza aiwatar da yarjejeniyar 2025 tsakanin gwamnati da kungiyar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262