Kura da Shan Bugu: Jagororin APC Sun Ga Laifin Tinubu kan Naɗa Tegbe Minista
- Jagororin jam'iyya mai mulki ta APC a Oyo sun yi fatali da nadin Joseph Tegbe a matsayin minista da Bola Tinubu ya yi
- Sun bayyana matukar takaici game da nadin, inda suka ce an tauye haƙƙin ‘yan jam’iyya masu biyayya da suka yi aiki don nasarar Tinubu
- Sun buƙaci Shugaba Tinubu da Majalisa su sake duba nadin domin a kwantar da hankulan ƴan jam'iyya da suka yi wa APC hidima
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo – Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Oyo sun nuna rashin amincewarsu da nadin Joseph Tegbe a matsayin wanda zai wakilci jihar a majalisar ministoci.
Akeem Adetoyese da Mogaji Abiola Oyeyemi sun bayyana hakan a cikin wata sanarwa da suka fitar, inda suka ce nadin tamkar rashin adalci ne ga ƴan jam’iyyar da suka yi wa Bola Tinubu aiki.

Source: UGC
Jaridar The Guardian ta wallafa jagoranci sun ce wannan nadi ya haifar da damuwa a tsakanin ƴan jam’iyya na matakin ƙasa da kuma tsofaffin masu biyayya a APC a jihar Oyo.
Ƴan APC sun fusata da naɗin Tinubu
Jagororin sun bayyana cewa naɗa Tegbe da Tinubu ya yi tamkar miƙa ladan aiki ne ga wanda ba yi komai ba, yayin da aka bar wadanda suka yi aikin a baya.
A cewarsu, akwai dimbin ‘yan APC da suka sadaukar da lokaci, kuɗi da kuma tsarin siyasa domin tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023, amma har yanzu ana watsi da su wajen rabon mukamai.
Sun kara da cewa nadin Tegbe na aika sako mara kyau ga ƴan jam’iyyar da suka tsaya tsayin daka tun kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe.

Source: Instagram
Sanarwar ta ce:
"Tsarin lada na jam’iyyarmu a Jihar Oyo na kara zama abin takaici. Akwai ‘yan jam’iyya da suka yi aiki dare da rana, suka tara dukiyarsu domin samun nasarar Shugaba Bola Tinubu, amma ana watsi da su.”
Zargin manyan APC kan Tegbe
Jagororin biyu sun zargi Tegbe da rashin nuna cikakkiyar biyayya ga APC, tare da cewa bai taka muhimmiyar rawa wajen nasarar jam’iyyar a jihar ba.
Sun kuma ce Tegbe ya taba yin takara a wata jam’iyya daban, tare da zargin cewa ya yi aiki da ya saba da burin Tinubu a zaɓen 2023.
A cewarsu:
“A bayyane yake cewa Tegbe ba wai kawai ya yi takara a wajen APC ba, har ma ya yi aiki da ya saba da nasarar Shugaba Tinubu. Wannan ya sa nadin nasa ya zama abin tambaya kuma rashin adalci ga masu biyayya.”
Sun kuma yi zargin cewa har yanzu Tegbe bai kammala rajista a matsayin cikakken ɗan APC ba, kuma bai halarci wasu muhimman tarukan jam’iyyar a jihar ba.
Jiga-jigan jam’iyyar sun gargadi cewa ci gaba da watsi da masu biyayya na iya haifar da rashin jin daɗi a matakin ƙasa, wanda hakan zai iya raunana jam’iyyar gabanin zaɓuka masu zuwa.
Tinubu ya naɗa Tegbe minista
A baya, mun ruwaito cewa majalisar ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samu sabon minista biyo bayan nadin da aka yi a baya-bayan nan.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon Ministan lantarki wanda zai maye gurbin Adebayo Adelabu sakamakon murabus din da ya yi domin neman takara.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauko Joseph Olasunkanmi Tegbe wanda ya fito daga jihar Oyo, ya ba shi mukamin ministan makamshi na tarayyar Najeriya.
Asali: Legit.ng


