Ibrahim Yusuf
5317 articles published since 03 Afi 2024
5317 articles published since 03 Afi 2024
China ta kakaba wa wasu kamfanonin Amurka takunkumi tare da tsaurara dokar fitar da drones, tana mai cewa martani ne ga matakan da Washington ta ɗauka kan Beijing.
ECOWAS ta buɗe neman shiga shirin horas da matasa masu digiri na 2027, inda ƴan Najeriya masu shekaru 32 zuwa ƙasa za su iya samun aikin shekara daya.
Donald Trump ya caccaki Abdul El-Sayed bayan ya lashe tikitin takarar Sanata na Democrat a Michigan, yayin da El-Sayed ya yi kira ga haɗin kan jam'iyya.
Sojojin Isra'ila sun harba makami kan nasu dakaru a Lebanon bisa kuskure, yayin da aka kama 'yan mata 10 da suka tsallaka iyaka domin kafa matsugunan Yahudawa.
Khalifa Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya kai wa Shugaba Tinubu goron gayyatar babban Mauludin Sheikh Ahmad Tijjani da za a gudanar a Kano ranar 9 ga Agusta, 2026.
NiMet ta yi hasashen hadari da ruwan sama na kwanaki uku a Najeriya, tare da gargadin jama'a su yi taka-tsantsan saboda iska mai ƙarfi da ambaliyar ruwa.
Abdul El-Sayed ya lashe tikitin Sanatan Democrats a Michigan bayan ya doke Haley Stevens, kuma zai fafata da Mike Rogers a zaɓen Nuwamba mai muhimmanci.
Nyesom Wike ya ce Cardinal Onaiyekan ba ya nuna tsaka-tsaki kan siyasa, yayin da Ƙungiyar Matasan Arewa da Middle Belt Forum suka fito suka kare malamin.
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya sanar da taron International Conference na Izala a Abuja tare da gayyatar Sheikh Sani Yahaya Jingir, lamarin da ya jawo martanin jama'a.
Ibrahim Yusuf
Samu kari