Iran Ta Kakkabo Jirgin Yakin Amurka a Kusa da Mashigar Hormuz
- Rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kakkabo jirgin leken asirin Amurka kirar MQ-9 a mashigar ruwan Hormuz
- Iran ta kuma yi ikirarin cewa wannan shi ne jirgin MQ-9 na Amurka na 58 da sojojinta suka kakkabo tun bayan fara yakin da suka yi
- A wani bangaren kuma, Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa na fuskantar yakin tattalin arziki na boye da ya fi yakin makamai masu linzami wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran – Rahotanni daga Gabas ta Tsakiya sun nuna cewa Iran ta yi ikirarin kakkabo jirgin leken asirin Amurka kirar MQ-9 a sararin samaniyar mashigar ruwan Hormuz.
Iran ta bayyana cewa Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce rundunar tsaron sararin samaniyarta ce ta yi amfani da sabon tsarin kariyar sama wajen gano jirgin da kuma kakkabo shi.

Source: Getty Images
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa rundunar IRGC ta ce wannan shi ne jirgin MQ-9 na Amurka na 58 da sojojin Iran suka yi ikirarin kakkabowa.
korafin da Pezeshkian ya yi
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasarsa na fuskantar wani yakin tattalin arziki na boye wanda ya fi yakin da ake amfani da makamai masu linzami wahala.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito cewa Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin wani taro da masu zuba jari da masana’antu.
Shugaban ya ce wasu kasashe masu danniya da amfani da karfi suna kokarin durkusar da Iran, amma ya yaba wa ’yan kasuwar kasar bisa yadda suke tafiyar da harkokinsu duk da kalubalen da ake fuskanta.
Rahoto ya nuna cewa ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin tabbatar da cewa ba za ta bukaci katse wutar lantarki a lokacin hunturu ba.
An kai hari kan jiragen dakon mai
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce wani jirgin dakon mai da ke barin mashigar Hormuz ya gamu da hari da wani makami da ba a san ko wane ne ya harba shi ba.
Hukumar ta bayyana cewa makamin ya bugi dakin injin jirgin ne mai nisan mil 17 a teku, kwatankwacin kilomita 31 daga gabashin garin Khasab na kasar Oman.

Source: Getty Images
Sai dai rahotannin da aka fitar daga baya sun nuna cewa hukumar ta ce babu wanda ya samu rauni sakamakon harin.
Kafin wannan lamari, UKMTO ta ruwaito cewa wani jirgin dakon mai ya gamu da irin wannan hari mai nisan mil 11, kwatankwacin kilomita 20 daga arewacin Khasab.
Trump ya gana da Xi da Putin
A wani labarin, mun rahoto cewa shugaban China, Xi Jinping, ya bukaci a haramta makaman nukiliya gaba daya tare da lalata dukkan wadanda ake da su.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce hadin gwiwar kasashen Rasha, Amurka da China na iya taimakawa wajen karfafa zaman lafiyar duniya.
Shi kuwa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana taron shugabannin kasashen uku a matsayin wani abu da zai shiga tarihi.
Asali: Legit.ng

