Gwamnati Ta Kama ‘Yan Kasar Waje, An Rufe Su a Kurkuku kan Zargin Satar Mutane a Abuja
- Wata kotun tarayya ta yi umarnin tsare 'yan ƙasar Mali 11, ciki har da mata huɗu, bisa zargin garkuwa da mutane da kuma safarar bil'adama
- Gwamnati ta zarge su da sace Alfonseni Diakite da wasu mutane domin karɓar kuɗin fansa, tare da yaudararsu saboda sus amu abin duniya
- Dukkan waɗanda ake zargin sun musanta laifuffukan, yanzu kotun ta ɗage shari'ar zuwa ranar 26 ga Janairu 2026 domin fara sauraron ƙarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare wasu 'yan ƙasar Mali 11 a gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja.
Ana tuhumar waɗannan mutane ne bisa zargin hannu a satar mutane domin karɓar kuɗin fansa da safarar bil'adama, waɗanda suka saɓa doka.

Source: Getty Images
Ana zargin wasu mutanen Mali da yin garkuwa

Kara karanta wannan
2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna
Blueprint ta ce Obiora Egwuatu ne ya bayar da umarnin tsare su bayan waɗanda ake zargin sun musanta tuhume-tuhume huɗu da ake yi masu.
Mutanen da ake zargin sun haɗa da Abdul Ngeki, Ahmed Kasango, Hassan Dauda, Saidu Traore, Ahmed Sirama da wani Mohammed Dembele.
Sannan ana tuhumar Musa Sidibe, Fatima Coulibaly, Aisha Dembele, Habi Tohgo da Lah Ahmed.
Gwamnatin Najeriya ta zarge su da aikata laifuffukan a Babban Birnin Tarayya Abuja tsakanin watan Maris da Afrilun wannan shekara ta 2026.
Lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo SAN kuma Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya, ne ya shigar da sababbin tuhume-tuhumen a kotu.
Tuhumomin da ake yi wa waɗanda ake ƙara
A tuhuma ta farko, masu gabatar da ƙara sun zargi waɗanda ake tuhuma da haɗa baki wajen tsare Alfonseni Diakite da wasu mutane ba bisa ƙa'ida ba.
Rotimi Oyedepo SAN ya ce an tsare Diakite ne domin neman kuɗin fansa daga wajen iyalansu.
Gwamnati ta ce waɗannan tuhume-tuhumen sun saɓa sashe na 26(1) da 24(1)(a) na dokar hana ta'addanci ta shekarar 2022 a cewar Premium Times.
A tuhuma ta uku, an zarge su da haɗa baki wajen karɓar Diakite da sauran mutanen ta hanyar yaudara domin cin zarafinsu a samu dukiya da su.
Lauyan Gwamnatin Tarayya ya faɗa wa kotu ragowar tuhume-tuhumen sun saɓa wa sashe na 27 da 13 na dokar hana safarar mutane ta shekarar 2015.
An gurfanar da waɗanda ake zargi
Wata lauyar gwamnati, M.A. Oladunjoye, ta nemi kotun ta umarci a karanta wa waɗanda ake tuhuma laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa.
Lauyan waɗanda ake tuhuma, Steven Ogbadu, bai yi adawa da wannan buƙata ba. Daga bisani, an karanta musu tuhume-tuhumen kuma suka masu.
Da aka fassara masu abin da ake cewa zuwa harshen Faransanci ta hannun tafinta, dukkan mutane 11 sun musanta aikata waɗannan manyan laifuffuka.
An ɗaure 'yan ƙasar waje a gidan gyaran hali
Daga nan Oladunjoye ta nemi kotun ta sanya ranar fara shari'a tare da bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali na Suleja har zuwa lokacin shari'ar.
Da alƙalin ya tambayi dalilin zaɓar gidan gyaran halin Suleja, ta bayyana cewa gidan gyaran hali na Kuje ba ya karɓar mata, kuma aka yarda da hakan.
Lauyan waɗanda ake zargi bai yi adawa da buƙatar tsare su ba. Sai dai ya shaida wa kotun cewa tuni ɓangaren masu bada kariya sun nemi a sasanta.
Ana tattaunawa da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, domin warware matsalar ta hanyar yarjejeniyar amincewa da laifinsu.
Alƙalin ya amince da buƙatar tsare su a Suleja zuwa lokacin shari'a. Kotun ta ɗage shari'ar zuwa ranar 26 ga Janairu 2026 domin fara sauraron ƙarar.
Tarihin lambar yabon GCON a Najeriya
Shugabanni daga kan Nnmadi Azikiwe, Ibrahim Babangida zuwa Bola Tinubu sun karrama mutane har da na kasar waje da lambobin yabo a tarihi.
Cikin wadanda suka samu lambar akwai Atiku Abubakar, Aliko Dangote, Yemi Osinbajo da mutanen kasar irinsu Sarauniya Elizabeth da Narendra Modi.
Shugaba Bola Tinubu ya kara sunan fitaccen lauya Wole Olanipekun cikin jerin bayan karrama shi da lambar GCON a ranar Alhamis da ya cika shekara 75.
Asali: Legit.ng

