Ministan Tinubu Ya Ce Wutar Lantarki Ta Inganta a Najeriya, ana Masa Godiya
- Ministan makamashi, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa samun ingantuwar wutar lantarki ya sa wasu ƴan ƙasa roƙonsa ya rage ƙarfin wutar
- Rahoto ya nuna cewa Tegbe ya bayyana cewa an fara samun sa'o'i 18 na wutar lantarki a yankunan da a baya ba sa samu ko kadan
- Ministan ya nuna damuwa kan barnatar da kayan wutar lantarki da wasu ke yi game da kadarorin gwamnati a fadin kasar nan a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana cewa wasu aiki da wutar lantarki sun buƙaci da ya rage ƙarfin wutar sakamakon irin gagarumin ci gaban da aka samu a ɓangaren, yana mai cewa "firijinsu na daskarar da abubuwa sosai".
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta tsarin hasken rana mai ƙarfin megawatt 3 a Jami'ar Abuja, inda ya ce al'umma na amfana da irin sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta kawowa.

Source: UGC
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministan yana bayyana irin sauye-sauyen da aka samu a ɓangaren samar da wutar lantarkin.
Ya bayyana cewa:
"Wuraren da ba su samu wuta kwata-kwata na tsawon wata uku, yanzu suna samun wuta ta tsawon sa'o'i 18. Wasu ƙira na suka yi suna cewa, duba nan, ya kamata in rage ƙarfin wutar, domin komai da ke cikin firijinsu yana daskarewa."
Lalacewar kayan lantarki
Ministan ya amince da ƙalubalen da ke gaban ɓangaren, inda ya bayyana cewa yawancin kayayyakin lantarki a ƙasar sun wuce shekaru 40.
Haka zalika ya nuna damuwarsa kan yadda masu ɓarna ke cutar da kadarorin wutar lantarki, inda ya bayyana cewa an rushe manyan tasoshin wutar lantarki uku a Birnin Kebbi.

Source: Twitter
Sakamakon hakan, gwamnatin tarayya ta haɗa gwiwa da hukumomin EFCC, Ƴan sanda da NSCDC domin kare kadarorin wutar lantarki na ƙasar.
Vanguard ta wallafa cewa shugaban hukumar REA, Abba Abubakar Aliyu, da Shugaban Jami'ar Yakubu Gowon, Prof. Hakeem Fawehinmi, sun jaddada muhimmancin wutar lantarkin ga harkar ilimi.
Legit ta tattauna da Lawan
A wata tattaunawa da Lawan Musa da ke karamar hukumar Darazo da ke jihar Bauchi, ya bayyana cewa ba su samun wutar lantarki.
Lawan ya ce:
"Mu kam ba mu ga sauyi ba. Kamar ma dai ba a yi wani sauyi ba muke ji a nan kam.
"Akwai bukatar ministan ya yi yawo zuwa wasu wurare ya ga yadda ake fama da matsalar wutar lantarki."
Sowore zai inganta lantarki
A wani labarin daban, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi alƙawarin gabatar da mafi ƙancin albashi na N500,000 ga ma'aikatan Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.
Ɗan fafutukar ya kuma bayyana cewa jam'iyyarsa za ta samar da wutar lantarki ta tsawon sa'o'i 24, gami da maida ilimi kyauta a kowane mataki.
Sowore ya bayyana wannan alƙawari ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya bayyana tsarin jam'iyyar AAC na kawo sauyi na adalci ga ƴan Najeriya.
Asali: Legit.ng


