Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu game da Hari kan Rarara a Abuja

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Magantu game da Hari kan Rarara a Abuja

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara
  • Ahanotu ya ce goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ko bayyana ra’ayin siyasa haƙƙin dimokuraɗiyya ne
  • Ya buƙaci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP), Prince Kennedy Ahanotu, ya yi magana an hari da aka kai wa Dauda Kahutu Rarara.

Ahanotu ya yi Allah wadai da kai wa mawaƙin Hausa kuma mai goyon bayan jam’iyyar APC, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, hari a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.

Dan siyasa ya soki farmaki kan Rarara
Mawaki Dauda Kahutu Rarara da tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Kennedy Ahanotu. Hoto: Prince Kennedy Ahanotu, Dauda Kahutu Rarara.
Source: Facebook

Dan LP ya soki hari kan Rarara

Ahanotu, wanda kuma shi ne wanda ya kafa ƙungiyar Renewed Hope Alliance of Labour Party Youth Leaders (RHALY), ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Ya ce ƙungiyarsa ta ɗauki lamarin a matsayin abin damuwa matuƙa, musamman a lokacin da Najeriya ke buƙatar haƙuri da bambancin ra’ayin siyasa, haɗin kan ƙasa da kuma mutunta haƙƙoƙin jama’a ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba.

An dai zargi wasu mutane da kai wa mawaki Rarara hari saboda rashin jin daɗinsu da goyon bayan da yake bai wa jam’iyyar APC mai mulki da Shugaba Bola Tinubu.

A wani ɓangare na sanarwar, Ahanotu ya ce:

“Abin takaici ne matuƙa yadda wurin ibada, wanda ya kamata ya kasance cibiyar zaman lafiya, ’yan’uwantaka da mutunta juna, ya zama wurin aukuwar irin wannan mummunan rikici."
"Dole ne mu bayyana cewa goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda yake cikin jam’iyyar APC, ko bayyana ra’ayin siyasa haƙƙi ne na dimokuraɗiyya. Bai kamata a kai wa kowa hari, yi masa barazana, tsoratar da shi ko wulaƙanta shi a bainar jama’a saboda amfani da wannan haƙƙi ba.”

Kara karanta wannan

Matasa sun far wa wawakin siyasa, Dauda Rarara da duka a masallacin Juma'a

Ahanotu ya yi Allah wadai da hari kan Rarara
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da Kennedy Ahanotu. Hoto: Seyi Tinubu.
Source: Instagram

Gargadin da Ahanotu ya yi

Ahanotu ya gargaɗi cewa bai kamata a ɗauki haƙurin magoya bayan APC a matsayin rauni ba, cewar rahoton Daily Post.

Ya ce magoya bayan APC a faɗin Najeriya miliyoyi ne, kuma suna da ƙarfin tsari da dimokuraɗiyya wajen kare muradunsu na siyasa.

Sai dai ya jaddada cewa dole ne su nuna wannan ƙarfi ta hanyoyin da doka ta amince da su, cikin lumana da bin tsarin dimokuraɗiyya, ba ta hanyar ɗaukar fansa ko tashin hankali ba.

Ahanotu ya buƙaci mukaddashin Sufeto Janar na ’yan sanda, rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya kuma nemi a gano waɗanda suka aikata laifin tare da tabbatar da an yi musu adalci bisa tanadin doka.

Haka kuma, ya yi kira ga gwamnati da ta ƙarfafa tsaron ’yan siyasa, magoya bayan ’yan takara da sauran jama’a yayin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

Rarara: Jigon APC ya yi Allah-wadai

Mun ba ku labarin cewa tsohon mai neman takarar sanatan APC a Imo, Hon. Belusochukwu Enwere, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara.

Ya yi gargaɗin cewa tsoratarwa da tashin hankalin siyasa na iya kawo cikas ga dimokuraɗiyya gabanin zaɓen 2027.

Enwere ya buƙaci jami’an tsaro su binciki harin, gano waɗanda suka aikata shi tare da tabbatar da an hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.