'Yan Gwagwarmaya Sun Kaddamar da Tafiyar Kifar da Tinubu a 2027
- Wasu ’yan gwagwarmaya sun ƙaddamar da gangamin Tinubu Must Go (TMG) domin wayar da kan ’yan Najeriya kan burinsu na ganin an samu sauyin gwamnati a zaɓen 2027
- Lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ya bayyana cewa gangamin na ƙarfafa haɗin kan jam’iyyun adawa da magoya bayansu domin marawa ɗan takara guda baya a zaɓen shugaban ƙasa
- Haka kuma, wasu masu goyon bayan gangamin sun fara yaɗa saƙonnin TMG a kafafen sada zumunta, yayin da suke kira ga shugabannin adawa su haɗa kai kafin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wasu ’yan gwagwarmaya a Najeriya sun fara gangamin da suka sanya wa suna Tinubu Must Go (TMG), wanda manufarsa ita ce wayar da kan jama’a kan bukatar samun sauyin gwamnati ta hanyar zaɓen 2027.
Lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima ya bayyana yadda tafiyar za ta yi aiki inda ya yi bayanin manufofin tafiyar da suke jagoranta.

Source: Facebook
Daya daga cikin jagororin gangamin, Hamza Nuhu Dantani, ya wallafa a Facebook cewa manufar TMG ita ce haɗa kan ’yan adawa da magoya bayansu domin samun ɗan takara guda da zai fafata a zaɓen shugaban ƙasa.
Manufofin gangamin TMG
A cewar Abba Hikima, tafiyar TMG ta yi imanin cewa wajibi ne jam’iyyun adawa da magoya bayansu su ajiye bambance-bambance domin haɗa kai.
A sakon da ya wallafa a Facebok, Abba Hikima ya ce ko da shugabannin adawa ba su cimma matsaya kan ɗan takara guda ba, magoya bayansu za su iya zaɓar wanda suka fi ganin zai iya wakiltarsu tare da marawa mutumin baya.
Abba Hikima ya kuma yi kira ga magoya bayan Atiku Abubakar da Peter Obi su matsa wa shugabanninsu domin su haɗa kai gabanin zaɓen 2027.

Source: Facebook
Dantani ya yi bayanin gangamin
Hamza Nuhu Dantani ya ce TMG ba ƙungiya ba ce mai tsarin shugabanci da muƙamai, illa wata tafiya ta wayar da kan jama'a.
Ya ce sun kafa gangamin ne saboda ba su gamsu da yadda gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da al’amuran ƙasa ba.
Dantani ya kuma bayyana cire tallafin man fetur a matsayin ɗaya daga cikin matakan gwamnati da suka jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Masu goyon bayan gangamin sun fara wallafa saƙonni da tambarin TMG a shafukan sada zumunta domin yaɗa manufarsu.
Sarkin Benin ya goyi bayan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya bayyana goyon bayansa ga yunƙurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027.
Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da tawagar kwamitin yakin neman zaɓen APC ta kai masa ziyara a fadarsa domin neman addu’a da goyon baya.
Oba Ewuare II ya ce masarautar Benin ba ta goyon bayan wata jam’iyya, amma ya tambayi dalilin sauya gwamnati saboda sauyi kawai ba tare da la’akari da ci gaba ba.
Asali: Legit.ng

