Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku ana Maganar Siyasar 2027
- Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta ziyarci ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar
- A bayanin da ya yi, Atiku ya ce ziyarar Aisha ta tuna wa masu neman shugabancin Najeriya muhimmancin fifita jin daɗi, mutunci da makomar ’yan ƙasar
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya yi amfani da ziyarar wajen yin magana kan tsadar rayuwa, tare da bayyana irin tattalin arzikin da ya ce zai gina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa kuma matar marigayi Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ziyara.
Atiku ne ya bayyana ziyarar a wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce ya ji daɗin karɓar tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar.

Kara karanta wannan
Mutuwa ta girgiza ɗan takarar gwamna, mutum 6 daga cikin mutanensa sun rasu lokaci 1

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da ziyarar ne a wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Laraba, 16 ga Satumban 2026.
Aisha Buhari ta ziyarci Atiku
Atiku ya ce ziyarar Aisha Buhari ta kasance mai muhimmanci, yana mai cewa ta tunasar da masu neman shugabanci kan nauyin da ke gabansu na fifita jin daɗin al’umma.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a tabbatar da mutunci da makomar ’yan Najeriya, musamman a lokacin da iyalai ke fuskantar ƙarin kuɗi domin rayuwa.
Aisha Buhari, wadda ta kasance mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, ta samu rakiyar ɗaya daga cikin ’ya’yanta mata da wasu makusanta.
Magana kan tsadar rayuwa
Atiku ya ce iyalai a sassa daban-daban na Najeriya na fama da ƙarin kuɗin abinci, sufuri, ilimi, kiwon lafiya da sauran abubuwan da ake buƙata a rayuwar yau da kullum.
Ya ce ’yan Najeriya sun cancanci tattalin arzikin da zai ba wa masu aiki tuƙuru damar samun sakamako, ya buɗe damar ci gaba kuma ya bai wa kowa dan kasa damar rayuwa cikin mutunci.

Source: Facebook
Atiku ya yi alkawari
Atiku ya ce zai mayar da hankali wajen gina tattalin arzikin da zai bai wa ’yan Najeriya damar dogaro da kansu tare da samun rayuwa mai inganci.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
“’Yan Najeriya sun cancanci tattalin arzikin da zai gina su, ya dawo da damar ci gaba kuma ya ba kowane iyali damar rayuwa cikin mutunci da fatan cigaba. Wannan ita ce Najeriya da ya kamata mu gina tare, ƙasar da za ta sake yi wa jama’arta aiki.”
Duk da cewa Atiku ya bayyana cewa ya karɓi Aisha Buhari, bai bayyana takamaiman dalilin da ya sa tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai masa ziyara ba.
Atikuza ba Tinubu sammaci
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC na mika wa Shugaba Bola Tinubu takardun shari’ar da suka shigar ta hannun jam’iyyarsa ta APC.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da umarnin ne bayan sauraron bukatar Atiku ta neman a yi amfani da madadin hanyar mika takardar, yayin da aka samu matsala wajen mika ta kai tsaye ga Tinubu.
Atiku da ADC suna kalubalantar cancantar Tinubu na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, inda suka gabatar da zargin cewa an gabatar da wata takardar shaidar kammala NYSC da ake zargin ba ta sahihiya ba ga INEC.
Asali: Legit.ng

