Rikicin Wike da Gwamnonin APC Ya Isa Kasar Faransa, za masu Sulhu a Can
- Shugaba Bola Tinubu na shirin shiga tsakani a rikicin da ya kunno kai tsakanin wasu gwamnonin APC da Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Ana sa ran Tinubu zai gana da ɓangarorin biyu domin sasanta bambance-bambancen da ke tsakaninsu gabanin zaɓen 2027 a Faransa
- Rikicin ya ƙara ƙamari ne bayan Wike ya ci gaba da tallata ƙawancen Rainbow, yayin da gwamnonin APC suka ce ba za su goyi bayan shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaba Bola Tinubu na shirin shiga tsakani domin sasanta rikicin da ke tsakanin wasu gwamnonin jam'iyyar APC da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ana sa ran tattaunawar za ta gudana a ƙasar Faransa kafin ƙarshen wannan mako, inda Tinubu yake hutu a halin yanzu.

Source: Twitter
Tinubu zai shiga tsakani
Punch ta wallafa cewa Tinubu zai yi ƙoƙarin sasanta ɓangarorin biyu domin kawo ƙarshen saɓanin da ke tsakaninsu da kuma tabbatar da cewa ba sa yin aiki sabanin juna gabanin zaɓen 2027.
Rikicin ya shafi wasu gwamnonin APC da Wike, wanda duk da cewa yana jagorantar ma'aikatar gwamnatin APC, har yanzu yana daga cikin manyan 'yan jam'iyyar PDP.
Wike ya zargi gwamnonin APC
Wike ya zargi gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da takwaransa na Imo, Hope Uzodimma, da kasancewa a dalilin wasu ƙalubalen siyasar da yake fuskanta.
Ya ce adawar da wasu gwamnonin ke nuna masa na da alaƙa da yaɗuwar Rainbow Coalition, wanda yake cewa yana bai wa 'yan siyasa damar fafatawa da 'yan takarar APC a zaɓukan gwamna da na majalisar dattawa.
Wike ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba ya nufin zai goyi bayan dukkan 'yan takarar APC a jihohi.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis
Gwamnonin APC sun yi martani
Uzodimma, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC, ya bayyana cewa gwamnonin jam'iyyar ba za su goyi bayan duk wani ƙawance ko tsarin siyasa da zai raunana APC ko ya kawo cikas ga sake zaɓen Tinubu ba.
Ya ce gwamnonin APC sun mayar da hankali ne wajen tallafa wa 'yan takarar jam'iyyar a dukkan matakan zaɓe.

Source: Twitter
Wike kuwa ya ce yana da 'yancin tallafa wa duk ɗan takarar da yake so, tare da jaddada cewa Rainbow Coalition na tallafa wa Tinubu ne a zaɓen shugaban ƙasa, yayin da PDP za ta iya fafatawa a sauran zaɓukan.
Wasu shugabannin APC sun bayyana cewa rikicin ba ya tsaya kan zaɓen 2027 kawai, domin akwai kuma lissafin siyasar 2031 da kuma wanda zai jagoranci Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 11.
Martanin APC ga Wike
Shugabannin APC na Kudu maso Gabas sun kuma bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, da gwamnonin APC, tare da yin watsi da kalaman da Wike ya yi kan gwamnonin.
Shugabannin jam'iyyar sun nemi Wike ya janye kalaman da suka ce ba su dace ba, tare da yin kira da a koma ga ladabtarwar jam'iyya, mutunta juna da ɗaukar nauyin jama'a baki ɗaya.
The Cable ta rahoto sun ce ba za su amince da duk wani ƙawance da zai raunana tsarin APC a yankin ba, tare da jaddada goyon bayansu ga 'yan takarar jam'iyyar a zaɓen 2027.
Kofa ya yi gargadi kan Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan majalisar tarayya kuma jigon APC, Abdulmumin Jibrin, ya gargadi wasu gwamnonin jam'iyyar da ke nuna rashin jin daɗi kan Wike da su guji kunyata shi a bainar jama'a.
Jibrin ya bayyana cewa Wike na da muhimmiyar rawa wajen nasarar da APC ta samu wajen samar da shugabancin Bola Tinubu, yana mai cewa membobin jam'iyyar ba za su iya cewa ba su amfana da ƙoƙarinsa ba.
Ɗan majalisar ya ce Wike ginshiƙi ne ga APC, tare da bayyana cewa ya yi sadaukarwa mai yawa wajen tallafa wa Tinubu da jam'iyyar, don haka bai kamata a kunyata shi ba.
Asali: Legit.ng

