Abin Mamaki da Kwankwaso Ya Leko a Arewa Maso Gabas kan Takararsa da Obi

Abin Mamaki da Kwankwaso Ya Leko a Arewa Maso Gabas kan Takararsa da Obi

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce saƙon fatan alheri na jam’iyyar NDC da haɗin gwiwarsa da Peter Obi na samun karɓuwa a Arewa
  • Kwankwaso ya bayyana haka ne bayan rangadin kwanaki huɗu da ya kai Gombe, Potiskum, Damaturu da Maiduguri
  • Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce jam’iyyar za ta farfaɗo da tattalin arzikin yankin ta hanyar ƙarfafa ƙananan sana’o’i da tattalin arzikin al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ya magantu kan ziyararsa a Arewa maso Gabas.

Sanata Kwankwaso ya ce saƙon fatan alheri na jam’iyyar na samun karɓuwa a yankin Arewa maso Gabas.

Kwankwaso ya kai ziyara Arewa maso Gabas
Dan takarar mataimakin shugaban kasa a NDC, Rabiu Kwankwaso da Buba Galadima a ganawarsu da jama'a a Borno. Hoto: @KwankwasoRM.
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a X bayan kammala rangadin kwanaki huɗu da ya gudanar a yankin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Tsohon gwamnan ya ziyarci Gombe, Potiskum da Damaturu a jihar Yobe, kafin ya isa Maiduguri, jihar Borno.

Ya ce rangadin ya ba shi damar tattaunawa da al’ummar yankin tare da jajanta musu bisa matsalar rashin tsaron da ke ci gaba da addabar wasu sassan jihohin Yobe da Borno.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa haɗin gwiwar siyasa ta Obi-Kwankwaso da jam’iyyar NDC sun kuduri aniyar magance matsalolin da yankin ke fuskanta tare da dawo da harkokin tattalin arzikinsa.

A cewarsa, jam’iyyar na da shirin farfaɗo da tattalin arzikin yankin ta hanyar ƙarfafa ƙananan hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga da kuma tallafa wa harkokin kasuwanci a matakin al’umma.

Kwankwaso ya ce:

“Ina farin cikin sanar da cewa saƙon fatan alheri na Obi-Kwankwaso da NDC yana samun karɓuwa. Mun jajanta wa al’ummar jihohin Yobe da Borno musamman kan matsalar rashin tsaron da ke ci gaba da addabar rayuwar mutane da dama.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

Kwankwaso ya fadi matsalolin Arewa maso Gabas
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya yaba wa Peter Obi

Ya ƙara da cewa haɗin gwiwarsa ta siyasa za ta yi ƙoƙari sosai wajen dawo da harkokin tattalin arziki a yankin da kuma inganta rayuwar mazauna yankin.

Haka kuma, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya yabawa ɗan takararsu na shugaban ƙasa, Peter Obi, bisa abin da ya bayyana a matsayin gagarumin aikin da yake gudanarwa a jihar Anambra da sauran sassan ƙasar nan.

Kwankwaso ya ce:

“Haka kuma, abin farin ciki ne ganin yadda kuma ɗan takararmu na shugaban ƙasa a NDC, mai girma Peter Obi, yake gudanar da ayyuka masu kyau a jihar Anambra da sauran sassan ƙasar nan.”

Rangadin Kwankwaso a Arewa maso Gabas na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu ke ƙara zage damtse wajen gudanar da shawarwari da neman goyon bayan jama’a gabanin babban zaɓen 2027.

Gombe: Kwankwaso ya zargi hana shi wurin taro

Kara karanta wannan

An yi wa Kwankwaso ba dadi da ya shiga Gombe, ya soki gwamnatin jihar

Mun ba ku rahoton cewa Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin jihar Gombe da matsa wa masu wani wurin taro lamba, lamarin da ya tilasta sauya wajen gudanar da taro.

Kwankwaso ya jagoranci taron tattaunawa da al’ummar Gombe ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026.

Jagoran Kwankwasiyya ya kuma gana da ’yan takarar jam’iyyar a jihar, tare da karɓar ziyarar dattawan ƙungiyar ci gaban Yamaltu Deba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.