An Saki Hotunan Barnar da Iran Ta Yi wa Amurka, an Lalata Jirage da Gine Gine
- Hotunan da aka fitar sun nuna irin gagarumar lalacewar da aka yi wa sansanonin sojin Amurka a ƙasashe irin su Saudi Arabia da Kuwait
- Sojojin Amurka sun nuna takaicin yadda ba a bayyana wa jama'ar kasar ainihin asarar da aka tafka a sansanoninsu ba
- Rahoton ma'aikatar tsaro ya tabbatar da cewa sojojin Amurka sun tafka asarar kayan aiki na dalar Amurka biliyan 3.7
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre me a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Hotunan da aka fitar kwanan nan sun tonar da asirin irin babbar lalacewar da hare-haren ƙasar Iran suka yi wa wurare da cibiyoyin sojojin Amurka daban-daban a yankin Gabas Tsakiya.
Rahoto ya nuna cewa an samu waɗannan hotuna daga hannun sojojin da ke tsaka da gudanar da ayyukansu, inda hotunan ke ɗauke da hotunan jirajen ruwa, gine-gine da sansanonin soji da aka tarwatsa.

Source: Facebook
Tashar BBC ta ruwaito cewa an ɗauki waɗannan hotuna ne a sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen Saudi Arabia da Kuwait.
Barnar da Iran ta yi wa Amurka
Ɗaya daga cikin sojojin da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya nuna damuwarsa matuƙa game da yadda gwamnatin Amurka ke ɓoye ainihin abin da ke faruwa.
CBS ta rubuta cewa:
"Wannan babbar lalacewa ce aka yi wa sansanoninmu wadda ba a sanar da jama'ar Amurka ba. Muna tsaye a nan muna ganin barnar da aka mana."

Source: Facebook
Iran ta lalata jirajen sa ido
Ɗaya daga cikin hotunan ya nuna yadda aka fasashe wani jirgin leƙen asiri na Boeing E-3 Sentry gida biyu a sansanin sojin saman Prince Sultan da ke Saudi Arabia.
Tsohon jami'in tsaron ƙasa Brian Katulis ya bayyana cewa lalacewar da aka gani a hotunan ta tabbatar da cewa Amurka ba ta shirya tsarin kariyarta da kyau ba.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun kashe yan ta'adda sama da 1000 a jiha 1 da ke Arewacin Najeriya
Katulis ya ƙara da cewa akwai alamun da ke nuna cewa abokan hamayyar Amurka kamar China da Russia sun taimaka wa Iran wajen gano wuraren da za ta kai harin.

Source: Facebook
Rahoton gudanarwa na Pentagon ya gano cewa hararen Iran sun lalata daruruwan gine-gine, tare da janyo asarar kayan aiki na dalar Amurka biliyan 3.7, yayin da Amurka ta kashe dalar Amurka biliyan 33.4 a yaƙin zuwa ranar 29 ga Yuni.
Za a tsayar da yakin Iran
A wani labarin daban, kun ji cewa majalisar wakilan Amurka ta ƙuri'a a karo na uku domin kawo ƙarshen yaƙin Iran, biyo bayan rahoton ofishin kasafin kuɗi na majalisa da ya nuna cewa yaƙin ya ci dalar Amurka biliyan 38.
Rahoto ya nuna cewa makaman kariya na kasar Amurka sun yi kasa sosai ta yadda za a ɗauki shekaru biyar kafin a sake tara su a yadda suke a da.
Wannan mataki da majalisar ta ɗauka na zuwa ne daf da zaɓen Nuwamba na kasar, inda tsadar rayuwa da kuma yaƙin ake sa ran za su shafi damar jam'iyyar Republicans a zaɓen.
Asali: Legit.ng
