Tinubu, Atiku, Obi da Sauran ‘Yan Takara Za Su Yi Muhawarar Zaben Shugaban Kasa
- An gayyaci Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi da wasu 'yan takara zuwa muhawarar shugaban kasa
- Masu shirya taron sun ce muhawarar za ta ba 'yan Najeriya damar tantance manufofi da shirye-shiryen 'yan takararsu
- Biyu daga cikin 'yan takarar shida ne suka tabbatar da halartar muhawarar da za a yi ranar 10 ga Janairu a birnin Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - An gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da Peter Obi zuwa wajen muhawara.
Manyan ‘yan takara shida da suke neman zama shugaban Najeriya aka shirya wa muhawara gabanin zaben 2027 domin su kara da junansu.

Source: Facebook
PIG ta shirya muhawarar 'yan takaran shugaban kasa
Kungiyar Political Intelligence Group (PIG) ta Politico.ng ce ta sanar da shirinta na gudanar da muhawarar kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan
Jita jita ta ƙare, an bayyana abin da aka tattauna tsakanin Peter Obi da 'yan Majalisar Amurka
Za a yi muhawarar ne a ranar 10 ga Janairu, 2027, a otal din Transcorp Hilton da ke birnin Abuja.
Shugaban kungiyar, Lai Omotola, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Legas ranar Juma'a, 20 ga watan Nuwamba 2026.
Sauran 'yan takarar da aka gayyata sun hada da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda ke takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC.
An gayyaci tsohon Gwamnan Cross River, Donald Duke wanda yake neman shugaban kasa a PRP; da kuma ‘dan takaran SDP, Adewole Adebayo.
Muhawarar 'yan takarar shugaban kasa a Najeriya
Omotola ya ce an shirya muhawarar ne domin ba 'yan kasa damar tantance manufofin 'yan takarar kuma su kwatanta shirye-shiryensu da za su kawo.
Muhawarar za ta ba talakawa fahimtar irin shirin da ‘yan siyasar suke da shi na jagorantar kasar.
The Sun ta rahoto shugaban na Politico.ng ya bayyana cewa zaben 2027 na iya zama daya daga cikin zabuka mafi muhimmanci a tarihin Najeriya,
Saboda haka ya ce ya kamata muhawarar ta zama wani bangare na tsarin dimokuradiyyar kasar.
'Yan takara ba su ba muhawara muhimmanci a yau
Ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karancin muhawarar 'yan takarar shugaban kasa, sai dai mutane su zabi shugabanni ba tare da sauraronsu ba.
Omotola ya tuna cewa an gudanar da muhawarar farko a shekarar 1993 tsakanin marigayi MKO Abiola na SDP da Bashir Tofa da ya nemi mulki a NRC.
Ya ce tun daga lokacin zuwa yanzu, Najeriya ta gudanar da muhawarar shugaban kasa sau takwas kacal, lamarin da ya bayyana a matsayin koma-baya.
A cewarsa, muhawarar za ta ba masu kada kuri'a da ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba damar yanke shawara idan suka ji saurare su kai tsaye.
Ya aka shirya muhawarar zaben na 2027?
An tsara gudanar da muhawarar na tsawon sa'o'i uku, inda za a raba ta zuwa sassa biyar.
Za a yi amfani da tsare-tsare daban-daban, ciki har da damar yin mu'amala da masu kallo ta kafafen sadarwa, kuma masu takara za su mike tsaye ko su zauna.
A karkashin tsarin, kowane dan takara zai samu mintuna biyar domin amsa tambaya, sannan a ba shi karin mintuna biyu domin yi wa abokin karawarsa raddi.
Omotola ya ce an tsara muhawarar ne bisa ka'idojin da ake amfani da su a kasashen duniya, yana mai fatan cewa zaman zai ja hankalin al'ummar duniya.
Domin tabbatar da gaskiya da adalci, ya ce za a kafa kwamitoci guda biyar da za su kula da shirya taron, inda kowanne dan takara zai zabi wakilinsa a cikinsu.
Zuwa yanzu dai an tabbatar da cewa ‘yan takara biyu sun amsa goron gayyatar wannan muhawara.

Source: Twitter
Babban kusa a NDC ya soki Bola Tinubu
Ana da labari cewa Injiniya Buba Galadima ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da nuna bambanci wajen kare rayukan mutanen jihar Borno.
'Dan siyasar ya ce tun tuni an ceto daliban da aka sace a Oyo amma watanni kusan shida kenan ba a kubutar da yaran da aka sace a Borno ba.
Saboda haka Buba Galadima ya ce babu wani mutumin jihar da zai zabi Bola Tinubu sai mahaukaci domin an manta da mutanen Arewa ta gabas.
Asali: Legit.ng

